Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana matuƙar farin ciki da yadda ake samun ƙaruwa a yawan ɗaliban da ke karatun harkar harhaɗa magunguna, tare da samun shaidar zama ƙwararru daga jihohin Kano da Jigawa.
Pharm. Hon. Hashim Ubale Yusuf, wanda ɗan siyasa ne, tsohon ma’aikaci a Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), manomi kuma mai kamfanonin sayar da magunguna, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai. Ya yi jawabin ne a lokacin taron yaye ɗaliban Jami’ar Bayero da suka kammala karatunsu tare da karɓar shaidar zama ƙwararrun masu harhada magunguna na ƙasa, wanda aka gudanar a ranar Talata.
Ya ce abin farin ciki ne matuƙa ganin cewa kusan ɗalibai 53 ne suka samu wannan shaidar ƙwarewa, inda mafi yawansu suka fito daga jihohin Kano da Jigawa, tare da wasu daga jihohin makwabta.
Pharm. Hon. Hashim Ubale Yusuf ya ƙara da cewa wannan ci gaba abin yabo ne matuƙa, duba da yadda ake fama da matsalolin yawaitar magungunan jabu da kuma shaye-shaye, waɗanda ke barazana ga lafiyar al’umma.
Ya ce ɗaya daga cikin manyan dalilan faruwar hakan shi ne ƙarancin ƙwararrun masana a fannin magunguna.
Ya nuna cewa ƙaruwa da ake samu a yawan masana a wannan fanni zai taimaka matuƙa wajen rage waɗannan matsaloli, tare da fatan nan gaba adadin waɗanda za su kammala karatun ya ninku fiye da na bana.
A ƙarshe, Pharm. Hon. Hashim Ubale Yusuf ya bayyana cewa ilimin da ya samu a fannin harhaɗa magunguna ya kasance ginshiƙi a rayuwarsa, wanda ya buɗe masa ƙofofi da dama har ya kai ga matsayin da yake a yau.
Ya nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare da yi wa sabbin ƙwararrun da suka samu shaida fatan alheri, yana mai fatan iliminsu zai zama abin amfani gare su da al’ummar jihohin Kano da Jigawa, da ma ƙasa baki ɗaya.






