Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Kamfanin LEON Projects ya sami lambar karramawa saboda nuna ƙwarewa da inganci wajen gina ɗakin da aka tanada domin kafa sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani (MRI Scan) a Asibitin Kashi na Tarayya da ke Dala, Kano.
An ba kamfanin lambar karramawar ne a yayin bikin ƙaddamar da na’urar MRI da Gidauniyar NNPCL ta samar tare da girka ta a asibitin.
Manajan Daraktan kamfanin, Arc. Modibbo Adamu Abubakar, ne ya karɓi lambar karramawar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan karɓar lambar, ya ce tun da aka ba su aikin sun yi alƙawarin gudanar da shi cikin ƙwarewa da inganci, domin sun san aikin zai amfani al’ummar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Ya ce, “Mun gina ɗakin da za a girka na’urar MRI tare da kammala aikin cikin lokaci. Yau kuma an karrama mu saboda gudummawar da muka bayar. Wannan ya nuna cewa duk wani aiki nagari da mutum ya yi, Allah yana gani, al’umma ma suna gani. Wannan karramawa babbar nasara ce a gare mu, kuma za ta ƙara mana ƙaimi wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima.”
Arc. Modibbo ya bayyana cewa an ba su wa’adin makonni huɗu ne domin kammala aikin gyaran da kuma shirya wurin da za a kafa na’urar, amma suka yi iya ƙoƙarinsu wajen kammala aikin cikin lokacin da aka tsara.
Ya kuma bayyana cewa aikin kafa irin wannan na’ura yana buƙatar ƙwarewa ta musamman, domin ana sa ido kan dukkan matakan aikin tun daga tushe har zuwa bangarorin ginin.
A cewarsa, kamfanin LEON Projects zai ci gaba da bayar da gudummawa ga ayyukan ci gaba da za su taimaka wajen bunƙasa harkokin lafiya da sauran fannoni masu muhimmanci a ƙasar nan.







