Abdulaziz Abdulaziz Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Malam Abdul’aziz Abdul’aziz, ya wakilci Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Malam Haruna, wanda aka yi wa matarsa da ’ya’yansa kisan gilla a jihar Kano.

A yayin ziyarar, Malam Abdul’aziz ya miƙa saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga iyalan marigayan, tare da nuna alhini da Allah wadai da wannan mummunan lamari.

Ya kuma tabbatar musu da cewa Shugaban Ƙasa ya bayar da umarni na musamman ga hukumomin tsaro domin gaggauta bincike tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan ta’asa, kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.

Haka kuma, Malam Abdul’aziz ya kai wata ziyarar ta’aziyya dangane da rasuwar Bature Abdulaziz, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata.

A ziyarar, ya miƙa ta’aziyya ga iyalai, ’yan uwa da abokan arziƙi a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya ji ƙan marigayin da sauran mamatan, ya gafarta musu, tare da bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani