Dagacin Gama Alhaji Rabiu Isyaku Shugaba Ne Mai Karrama Jama’a Da Zumunci -Yusuf Adamu Bello

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana cewa an samu gagarumin zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummomi da ƙabilu mabambanta da ke zaune a garin Gama, da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano ne sakamakon kyakkyawan jagorancin Dagacin Gama, Alhaji Rabiu Isyaku, tun bayan naɗa shi shekaru 25 da suka gabata.

Mai Unguwar Gwagwarwa, kuma maƙoci ga Dagacin Gama, Alhaji Yusuf Adamu Bello, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ’yan jarida a taron bikin cikar Dagacin Gama shekaru 25 a kan mulki.

Ya ce dukkan ƙabilun da ke zaune a yankin suna rayuwa cikin fahimta da mutunta juna, inda Dagacin ya rungume su tare da nuna musu muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, lamarin da ya sa ba su da wata fargaba a zamantakewarsu.

A cewarsa, “Dagacin Gama shugaba ne mai girmama jama’a da kula da zumunci. Idan wani al’amari ya taso, ko na farin ciki ko na akasin haka, zai zo da kansa ya taya ka murna ko alhini.”

Mai Unguwar ya ƙara da yi wa Dagacin Gama fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya saka masa da alheri bisa irin nasarorin da ya samu a cikin waɗannan shekaru 25, tare da roƙon Allah Ya ƙara masa ƙarfi da nasara a gaba.

Haka kuma, ya yi addu’ar Allah Ya bai wa al’ummar yankin Gama, ƙaramar hukumar Nasarawa da ma jihar Kano baki ɗaya zaman lafiya mai ɗorewa.

Alhaji Yusuf Adamu Bello ya jaddada cewa al’ummar yankin suna ba Dagacin Gama da dukkan masu unguwannin da ke ƙarƙashinsa cikakken goyon baya da biyayya, bisa kyakkyawan shugabancin da suke gani a aikace.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani