Auwal Sani Rogo Ya Bai Wa ’Yan Jarida Haƙuri Kan Zargin Cin Zarafi

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Jami’i na musamman mai aiko da rahotanni ga Gwamnan jihar Kano, Auwal Sani Rogo, ya bai wa ’yan jarida haƙuri bisa zargin cin zarafi da aka danganta masa.

Gwamnatin jihar Kano tare da jami’in nata sun nemi afuwar ƙungiyar ’yan jarida masu aiki a kafafen sada zumunta na Intanet kan abin da ya faru da ɗaya daga cikin mambobinta.

Matakin ya biyo bayan wani zaman sulhu da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kira a yau Laraba domin daidaita al’amuran da suka lalace.

Taron sulhun ya samu halartar shugabannin Kano Online Media Chapel ƙarƙashin jagorancin Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo, da daraktocin ma’aikatar yaɗa labarai, tare da ɗan jarida kuma tsohon shugaban NUJ, Abdullahi Datti Arzai.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishina Waiya ya buƙaci Rogo da sauran jami’an gwamnati su riƙa kyautata alaƙa da ’yan jarida domin ci gaban jihar.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da kafafen yaɗa labarai, yana mai bayyana muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar, Ɗangambo, ya gode wa Kwamishinan bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen warware matsalar, yana mai cewa an daɗe ana samun irin waɗannan koke-koke kan halayyar jami’in, wanda ya sa suka ga dacewar a magance lamarin.

Ya bayyana abin a matsayin abin takaici, tare da jan hankalin jami’an gwamnati su fahimci rawar da ’yan jarida ke takawa da muhimmancin aikinsu a cikin al’umma.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam na cikin da wajen ƙasar suka yi Allah-wadai da abin da ya faru, tare da kira ga gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana fatan cewa wannan sulhu zai taimaka wajen inganta mu’amala tsakanin jami’an gwamnati da ’yan jarida, tare da hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani