Zargin Cin Mutuncin ’Yan Jarida Daga Wasu Muƙarraban Gwamnan Jihar Kano Na Ƙara Bayyana

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Duk da irin shaida da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ke samu na kyakkyawar mu’amala da yake da ita da ’yan jarida a jihar, ana ci gaba da samun zarge-zargen cewa wasu daga cikin manyan muƙarrabansa da ke riƙe da muƙaman da ya ba su na cin zarafin ’yan jarida.

’Yan jarida da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai sun fito fili suna zargin wasu jami’an gwamnatin da cin mutunci da kuma kai musu hari yayin da suke tsaka da gudanar da aikinsu. Waɗannan zarge-zarge sun jawo muhawara kan kariyar ’yancin aikin jarida a jihar.

Wani ɗan jarida, Mubarak Auwal, ya ce ya fuskanci cin mutunci daga wani jami’in gwamnatin jihar, Auwal Sani Rogo, a lokacin wani taron siyasa da ya shafi karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga tsohuwar jam’iyyarsa zuwa sabuwar jam’iyya.

Mubarak ya bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da yake gudanar da watsa shiri kai tsaye a gidan rediyon Hikima Radio, inda aka samu taƙaddama tsakanin jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta bayan an hana shi shiga wajen manyan baƙi.

Ya ce jami’in ya buƙaci ya dakatar da watsa shirinsa amma ya ƙi, yana mai cewa yana aiwatar da aikinsa na jarida ne.

Haka kuma, wani ɗan jarida mai ɗaukar hoto a gidan talabijin na Abubakar Rimi Television (ARTV) ya zargi wani jami’i da kai masa hari a bainar jama’a yayin bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kan Nijeriya da aka gudanar a Kano.

Ya ce yana tsaka da ɗaukar hotunan bikin ne sai jami’in ya tunkare shi, ya tura shi ƙasa tare da zaginsa a gaban jama’a, ciki har da jami’an gwamnati da sauran ’yan jarida.

Ya bayyana abin a matsayin abin kunya da damuwa, musamman ganin cewa ya faru ne a wani babban taron gwamnati.

A wani lamari makamancin haka, an zargi mai taimaka wa Gwamna kan harkokin sadarwa, Ibrahim Adam, da wallafa hoton ɗan jarida Nazeer Bashir Tsamiya a shafukan sada zumunta, tare da tambayar abin da ya kamata a yi masa.

Rahotanni sun ce hakan ya biyo bayan binciken da aka yi kan zargin rashin zuwa aiki da wasu likitoci ke yi a wani asibiti a Kano, lamarin da ya tayar da muhawara kan kula da lafiyar marasa lafiya.

Tsamiya ya bayyana cewa wallafa hotonsa ya jefa rayuwarsa cikin barazana, yana mai cewa ya fuskanci tsangwama da barazanar kai masa hari bayan wallafa rahoton.

Masu sa ido kan harkokin yaɗa labarai na kira ga hukumomi su binciki zarge-zargen domin tabbatar da gaskiya da kuma kare ’yancin ’yan jarida yayin gudanar da aikinsu.

Sai dai wasu na ganin cewa irin waɗannan lamurra na rashin darajanta ’yan jarida daga wasu mukarraban gwamnati na ƙara tayar da tambayoyi kan matakin kariya da ake ba ’yan jarida a lokutan manyan taruka da al’amuran siyasa a jihar.

A gefe guda, ’yan jarida da dama sun yaba da kyakkyawar mu’amala da ke tsakanin Gwamnan jihar Kano da ’yan jarida, musamman ta hannun ofishin Daraktan Yaɗa Labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ake ganin yana da ƙwarewa a harkar jarida.

Wasu kuma na ganin cewa yawancin masu cusgunawa ’yan jarida na iya kasancewa sabbin masu riƙe muƙamai ne da ba su da gogewa wajen mu’amala da jama’a, inda suke kira ga gwamnati ta riƙa ba su horo kan hulɗa da kafafen yaɗa labarai.

Dangane da irin waɗannan zarge-zarge, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi Allah-wadai tare da kira da a binciki lamarin domin tabbatar da adalci.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani