Dakta Ganduje da Mai Ɗakinsa Farfesa Hafsat Jajirtattu Ne Wajen Hidimta Wa Addini -Malama Zahra’u Muhammad Umar

Daga Ibrahim Muhammad Kano
Fitacciyar malamar addinin Musulunci, tsohuwar babbar kwamandan mata ta Hukumar Hisba ta Jihar Kano, kuma tsohuwar Kwamishinar Ma’aikatar Mata, Malama Zahra’u Muhammad Umar, ta bayyana cewa Khadimul Islam Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tare da mai ɗakinsa Farfesa Hafsat, jajirtattu ne wajen yi wa addini hidima da kuma tallafa wa al’umma.

Malama Zahra’u ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da ‘yan jarida a taron buɗe masallaci da makarantar Islamiyya da Gidauniyar Ganduje ta gina a unguwar Bachirawa da ke Kano.

Ta ce, “Ban taɓa ganin mutum kamar Baba Ganduje ba, musamman ta fuskar hidimar gina masallatai. A cikin shekaru 10 da suka gabata mun ƙirga masallatai guda 46 da aka gina a garin Kano, kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu ba a san adadin waɗanda aka ƙara ba.”

Ta ƙara da cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tare da goyon bayan mai daƙinsa Farfesa Hafsat, suna ci gaba da gina masallatai da makarantu, da gudanar da ayyukan da’awa inda ake musuluntar da mutane, tare da shirye-shiryen kula da lafiya kamar aikin ido, bayar da magunguna ga cututtuka daban-daban, da kuma tallafa wa marasa galihu da sauran ayyukan alheri masu yawa.

Malama Zahra’u ta yi kira ga masu hali da su yi koyi da irin waɗannan ayyukan alkhairi, tana mai cewa gina makaranta da masallaci a unguwar Bachirawa — wadda ke da yawan jama’a — zai taimaka wajen koyar da ilimin addini da na boko, tare da rage wa gwamnati nauyi.

Haka kuma, ta buƙaci al’umma musamman masu hannu da shuni da su ƙara taimakawa marasa ƙarfi yayin da ake tunkarar watan Azumi, tana mai tunatar da cewa Manzon Allah (SAW) ya yi albishir da Aljanna ga masu taimakon mabuƙata da share wa mutane hawaye, kuma duk wanda ya sauƙaƙa wa wani a kan buƙatun rayuwa kamar abinci, sutura ko sufuri, Allah zai sauƙaƙa masa a ranar ƙiyama.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani