Gwamna Lawal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gwamnan Shekara Ta Jaridar LEADERSHIP

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na kawo sauyi mai ma’ana da farfaɗo da ƙwarin gwiwar al’umma ga harkokin mulki a jihar.

Gwamnan ya karbi Kyautar “Gwarzon Gwamnan Shekara” ta jaridar LEADERSHIP a ranar Alhamis, yayin taron shekara-shekara na jaridar da aka gudanar a Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa taron karramawar na LEADERSHIP na tantance fitattun mutanen da suka nuna ƙwazo da bajinta a fannoni daban-daban, tare da ba su lambar yabo bisa gagarumar nasarar da suka samu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Dakta Amina Mohammed ce ta zama babbar baƙuwa mai jawabi a kan taken taron na bana mai taken: “Tabbatar da Daidaiton Siyasa da Ci gaba Mai Ɗorewa a Afirka Cikin Tsarin Duniya Mai Cike da Ƙalubale: Hanyar Da Nijeriya Za Ta Bi.”

Sanarwar ta ce, karrama Gwamna Dauda Lawal a matsayin Gwamnan Shekara wata shaida ce da ke nuna irin gagarumin ci gaban da gwamnatin sa ta samu a sassa daban-daban a Zamfara.

Jaridar ta bayyana cewa, daga cikin dalilan da suka sa aka zabo shi, akwai ƙwazon jagoranci, jajircewa wajen ɗaukar matakai masu tsauri, da kuma aiwatar da shirye-shiryen sauyi da suka ɗora Zamfara kan turbar zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki da ci gaba mai ɗorewa.

An kuma nuna cewa bisa ginshiƙin kwarewa da nagartar aiki ne jaridar ta ga ya dace a karrama gwamnan da wannan babbar lambar yabo ta ƙasa.

Sanarwar ta tunatar da cewa irin waɗannan nasarori ne suka sa Gwamna Lawal ya samu Kyautar Gwamnan Shekara ta jaridar The Sun a watan da ya gabata, tare da Zamfara ta zama jiha ta farko a Arewa maso Yamma a gasar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa.

A cewar sanarwar, irin wannan karramawa za ta ƙara ƙarfafa gwiwar gwamnatin Zamfara wajen zurfafa tsaro, habaka noma da raya karkara, faɗaɗa ayyukan more rayuwa, inganta kiwon lafiya, bunkasa ilimi da kuma ƙarfafa jarin ɗan Adam a faɗin jihar.

  • Related Posts

    Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Jinjina Wa Gwamnan Zamfara

    Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana cewa Jihar Zamfara yanzu ta zama mai sauƙin isa ga masu zuba jari da abokan hulɗa, tare da jaddada cewa…

    Al’ummar Kano Ta Arewa Sun Yi Gangamin Neman Gwarzo Ya Fito Takarar Sanata

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Al’ummar yankin Kano ta Arewa sun gudanar da wani gangami domin nuna buƙatarsu ga Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da ya fito takarar sanatan yankin a…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani