Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mai neman tsayawa takarar kujerar Majalisar Jiha daga Ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Hussaini Lili Gabari, ya kai ziyarar girmamawa ga jigon jam’iyyar APC, kuma shugaban jam’iyyar siyasa ta Gangariya na kasa, Hon. Ado Tati, domin neman hadin kai da goyon baya gabanin zaben 2027.
A yayin ziyarar, Lili Gabari ya bayyana cewa yana gudanar da wani rangaɗi ne na musamman ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, domin gabatar da kansa tare da neman goyon bayansu.
Ya ce burinsa shi ne ganin jam’iyyar APC ta kasance cikin haɗin kai daga tushe har sama, domin tabbatar da nasara a zaɓuka masu zuwa.
Ya ƙara da cewa ba za a samu nasara ba sai an haɗa kan dukkan mambobin jam’iyyar, yana mai jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da kowa domin ƙarfafa jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, Hon. Ado Tati ya bayyana cikakken goyon bayansa ga takarar Lili Gabari, inda ya siffanta shi a matsayin ɗan siyasa mai ƙwarewa, jajircewa, da manufofi masu amfani ga al’umma.
A cewarsa, “Ina da cikakken yaƙini cewa Lili Gabari ya cancanci ya wakilci al’ummar Dala a Majalisar Jiha. Ina tare da shi ɗari bisa ɗari.”








