Makarantar Raudatuttanzeel Dukawuya Ta Yi Taron Yaye Mahaddata Alƙur’ani 11

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Makarantar Raudatuttanzeel da ke Unguwar Dukawuya ta gudanar da bikin yaye ɗalibai guda 11 na farko da suka sauke haddar Alƙur’ani mai girma tun bayan kafuwar makarantar.

Shugaban makarantar, Malam Musa Amir Salihu, ya bayyana cewa an kafa makarantar ne sakamakon haɗin gwiwar wasu matasa na unguwar Dukawuya da suka haɗu domin samar da mahaddatan Alƙur’ani a yankin.

Ya ce bayan tattaunawa da shawarwari ne aka kafa makarantar a shekarar 2018.

Ya ƙara da cewa a farkon fara karatun, an riƙa gudanar da darussa a wurare daban-daban kamar masallatai da harabar gidajen jama’a, kafin daga bisani a sami aron wani wuri a makaranta a unguwar, inda aka shafe kusan shekaru takwas ana gudanar da karatu har aka sami dalibai 11 da suka kammala hadda, aka shirya musu bikin yaye.

Malam Musa Amir Salihu ya ce daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta akwai rashin isasshen goyon baya daga wasu iyaye, da kuma wahalar da ake samu wajen jan hankalin wasu ɗalibai su dage wajen karatu. Ya ce duk da haka ana ci gaba da ƙoƙari domin cimma burin da aka sa gaba.

Ya yi kira ga iyaye da su riƙa ba da cikakken goyon baya domin tabbatar da samun yara masu haddar Alƙur’ani, yana mai cewa wannan nasara ce ga yara da iyayensu baki ɗaya.

Haka kuma ya buƙaci gwamnati da ta tallafa wajen bunƙasa karatun Alƙur’ani, domin hakan zai taimaka wajen inganta tarbiyya da ci gaban al’umma.

Shugaban makarantar ya ce babban burinsu shi ne tabbatar da cewa yara da suka haddace suna kiyaye haddarsu, su kuma zama abin koyi wajen karatun Alƙur’ani da sauran fannoni na ilimin addini, musamman tafsiri.

A nasa jawabin, Alhaji Haruna Idris Ahmad, wanda aka fi sani da Ɗanladi kuma uban makarantar, ya bayyana farin cikinsa da wannan gagarumar nasara.

Ya ce baya ga matsayinsa a makarantar, yana da ‘ya’ya uku daga cikin waɗanda suka haddace Alƙur’ani a makarantar, kuma yana roƙon Allah ya tsare musu haddarsu da tilawarsu.

Ya jaddada cewa akwai babban nauyi a kan iyaye wajen ci gaba da bibiyar karatun ‘ya’yansu, inda ya ce idan malamai sun yi nasu ƙoƙari, wajibi ne iyaye su ɗora ta hanyar tabbatar da yara suna maimaita abin da aka ba su na hadda a gida domin samun kyakkyawan sakamako.

Alhaji Danladi ya kuma bayyana cewa malamai na gudanar da aiki mai girma wanda babu wanda zai biya su hakkinsu sai Allah, yana addu’ar Allah ya saka musu da alheri da kuma ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Ya ƙara da cewa suna da burin faɗaɗa makarantar domin bai wa kowane yaro a unguwar damar samun ilimin Alƙur’ani ba tare da la’akari da halin kuɗi ba.

A yayin taron saukar Alƙur’ani, an raba takardun shaida da kyaututtuka ga malamai da ‘yan kwamitin makarantar, tare da karrama wasu masu bayar da gudummawa wajen bunƙasa makarantar.

  • Related Posts

    Iyaye da Gwamnati Su Ƙara Ba da Kulawa Ga Makarantun Alƙur’ani – Malam Mahmud TijjaniUsman Zangon Barebari

    Malam Mahmud Tijjani Usman Zangon Barebari ya yi kira ga iyaye da kuma gwamnati da su riƙa ba da kulawa ta musamman ga makarantun Alƙur’ani, domin inganta tarbiyyar yara da…

    Jami’ar Kebbi Ta Karrama Gwamna Lawal da Digirin Girmamawa

    Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero a Jihar Kebbi ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da digirin girmamawa na Dakta na Kimiyya (D.Sc Honoris Causa),…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani