Mun Rungumi Kwankwasiyya Ne Saboda Gaskiya Da Cigaban Al’umma -Danja

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kano, Hon. Isyaku Ali Danja, ya bayyana cewa sun rungumi tafiyar Kwankwasiyya ne saboda tsari ne na gaskiya, riƙon amana da kuma son ci gaban al’umma.

Danja, wanda ya ajiye muƙaminsa na mai bai wa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara, ya kuma koma jam’iyyar ADC, ya ce tsarin Kwankwasiyya tafiya ce da ake gudanarwa bisa gaskiya, inda idan aka samu nasara ake taimaka wa ‘ya’yan talakawa da kuma bunƙasa dukkan fannoni na rayuwar al’umma daga tushe.

Ya ce hakan ne ya sa talakawa suka rungumi tsarin Kwankwasiyya, yana mai cewa su ma sun shiga jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya ce tafiya ce da suka daɗe suna yi a siyasance.

Danja ya ƙara da cewa sun ɗan jinkirta ficewa daga gwamnati ne bisa umarnin jagoransu Kwankwaso, wanda ya bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Kwankwasiyya ce ta kafa ta, don haka masu muƙamai su ci gaba da zama domin kada a bai wa waɗanda ya kira azzalumai damar dawowa.

Sai dai ya ce an cimma lokacin da ya dace, wanda ya sa ya ajiye muƙaminsa domin ci gaba da tafiyar Kwankwasiyya kamar yadda aka tsara.

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC ta haɗa manyan ‘yan siyasa a faɗin kasar nan, yana mai cewa suna ganin ita ce mafita ɗaya tilo da za ta kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar APC a Nalijeriya da yardar Allah.

“A yau al’amari a bayyane yake tsakanin jam’iyyar APC da ake zargi da zaluntar jama’a, da kuma sabuwar jam’iyyar ADC da ake ganin za ta kawo ceton al’umma. Don haka ya rage ga talakawa su zabi abin da ya fi dacewa da su,” in ji shi.

Danja ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa sun kwashe mutane daga tsarin Kwankwasiyya, yana mai cewa taron da aka yi na komawar jagora Kwankwaso jam’iyyar ADC ya nuna irin goyon bayan da jama’a ke da shi, domin babu wanda aka bai wa kuɗi domin halartar taron.

Ya ƙara da cewa a wasu taruka kuwa, musamman na ƙasa a Abuja, ana zargin an ɗauki mutane aka kai su har suna kwana a kan titi duk da kasancewar suna da gwamnati.

“A bayyane yake cewa jama’a na tare da jagora Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma ba za su manta da alherinsa ba. Muna fatan shigarsa jam’iyyar ADC zai zama mataki na kawo karshen gwamnatin APC a kowane mataki,” in ji Danja.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani