Gwamna Lawal Sake Ya Lashe Lambar Yabo Ta Gwamnan Shekara A Landan

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu babbar karramawa a matakin ƙasa da ƙasa bayan da aka ba shi lambar yabo ta “Gwamnan Shekara” a bikin Fuskar Jagoranci a Afirka 2026, wato Face of Africa Leadership Award 2026, da aka gudanar a birnin Landan.

Wannan karramawa ta fito ne daga mujallar duniya ta Triangle Media International Magazine, wadda ke karrama fitattun shugabanni daga sassa daban-daban na duniya bisa irin tasirin da suke da shi a shugabanci da hidimar jama’a.

An gudanar da taron karo na goma na wannan muhimmin biki a babban zauren King’s College da ke Landan, inda manyan baƙi daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu suka halarta domin tattauna muhimmancin rawar da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke takawa wajen bunƙasa ci gaban ƙasa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa wannan lambar yabo ta 2026 ta zo ne daidai lokacin da mujallar ke bikin cika shekaru goma da kafuwa, tare da ci gaba da karrama fitattun ’yan Afirka masu tasiri.

Sanarwar ta jaddada cewa an ba Gwamna Lawal wannan karramawa ne bisa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, musamman a bangaren inganta ayyukan gwamnati da hidimar jama’a.

Kwamitin masu ba da kyautar ya bayyana cewa duk da halin matsin tattalin arziki da gwamnatin ta gada, Gwamna Lawal ya tsaya tsayin daka wajen aiwatar da manufofin “Ƙudurin Ceto” domin farfaɗo da jihar Zamfara.

Haka kuma, an yaba da dabarun da gwamnatin ke bi wajen rage matsalolin tsaro ta hanyar saka jari a fannin ilimi, ciki har da ayyana dokar ta-ɓaci a bangaren ilimi, da kuma biyan bashin kuɗaɗen jarrabawar WAEC da NECO da suka kai Naira biliyan 3.4.

Bugu da ƙari, an nuna yadda gwamnatin ta mayar da hankali wajen gyara da sake gina makarantu a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar, wanda aka bayyana a matsayin mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Taron ya samu halartar manyan baƙi ciki har da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da Babban Daraktan Kamfanin Sahara Group, Kola Adesina, tare da sauran fitattun mutane.

Wannan karramawa na ƙara tabbatar da matsayin Gwamna Lawal a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da ke kawo sauyi a Nijeriya, tare da ƙarfafa gwiwar gwamnatinsa wajen ci gaba da ayyukan ci gaba a jihar Zamfara.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo