Mun Samu Gagarumar Nasara Wajen Inganta Tsaron Kasuwar Ƙofar Wambai -Magajin Garin Kasuwa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Magajin Garin Kasuwar Ƙofar Wambai kuma shugaban kwamitin tsaron kasuwar, Alhaji Ibrahim Lawan Unguwar Ayagi, ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara wajen inganta tsaro a kasuwar, musamman wajen daƙile shigowar ɓarayi da masu aikata munanan ayyuka.

Ya ce musamman wasu mata da ke zuwa daga garuruwa daban-daban domin aikata sata da cutar da masu saye da sayarwa a kasuwar, an samu raguwar irin waɗannan ayyuka da kaso kusan 80 cikin 100 sakamakon sabbin matakan tsaro da aka dauka.

Alhaji Ibrahim Lawan Ayagi, wanda shi ne kuma mataimakin shugaban ƙungiyar ’yan ƙoli ta kasuwar, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce daga cikin matakan da suka ɗauka akwai samar wa masu kula da tsaron kasuwar kayan aiki na musamman da kuma samar da na’urorin amsa-kuwwa (walkie-talkie) domin sauƙaƙa sadarwa a tsakanin jami’an tsaron kasuwar.

A cewarsa, duk inda aka sami matsala ana iya sanarwa cikin gaggawa, kuma nan take a ɗauki matakin da ya dace.

Ya ce hakan ya taimaka matuƙa wajen inganta tsaro a kasuwar, musamman a wannan lokaci na hada-hadar kasuwanci a watan Azumi.

Magajin Garin ya ƙara da cewa Kasuwar Ƙofar Kofar Wambai ta shahara sosai, ba a jihar Kano ko Arewa kawai ba, har ma da sauran jihohin Nijeriya da ƙasashen Afirka, inda mutane daga wurare daban-daban ke zuwa domin sayayya.

Ya ce saboda yawan jama’ar da ke zuwa kasuwar, ana samun cunkoso sosai, amma duk da haka suna samun haɗin kai daga jami’an tsaro daban-daban wajen kula da tsaron kasuwar.

Ya kuma bayyana cewa a bara an samu cunkoso sosai a kasuwar har ma da kan titin IBB, wanda hakan ke kawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa. Sai dai a bana, duk da cewa akwai cunkoso, ana tafiya cikin tsari, mutane na ƙasa da masu ababen hawa na samun damar wucewa.

Ya danganta hakan da ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kano ke yi na faɗaɗa hanyoyi da inganta ababen more rayuwa, wanda ya taimaka wajen rage cunkoso.

Alhaji Ibrahim Ayagi ya ce ’yan kasuwa na nuna gamsuwa da matakan tsaro da kwamitin ke ɗauka, inda suke yaba wa matasan da aka ɗora musu alhakin kula da tsaron kasuwar.

Ya ƙara da cewa ana yawan samun kuɗaɗe ko wasu kayayyaki da suka ɓace a kasuwar, inda ake tattarawa a sanar domin a nemo masu su a mayar musu.

Haka kuma ya yaba wa uwar ƙungiyar kasuwar da kuma shugabannin ƙungiyoyin kasuwar bisa irin haɗin kai da goyon bayan da suke bayarwa, wanda ya ce yana taimakawa wajen ci gaban harkokin kasuwanci a kasuwar.

Magajin Garin ya kuma yaba wa masarautar kasuwar Ƙofar Wambai ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kasuwa, Alhaji Bashir, wanda a cewarsa shi ne ya assasa kwamitin tsaron kasuwar, kuma yake ci gaba da bayar da gudunmawa domin inganta tsaro da cigaban kasuwar.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani