Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta jihar Kano (ALGON), Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja, ta buƙaci hukumomin tsaro da ke jihar Kano da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan rikicin da ya ɓarke yayin rabon tallafin kayan Azumi a ƙaramar hukumar Tudun Wada, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami’in hukumar Civil Defence.
Rahotanni sun ce jami’in mai suna Buhari Mai Fulawa ya rasu ne a lokacin da ake rabon tallafin shinkafa da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya gudanar a yankin.
A wata sanarwa da ta fitar, Hajiya Sa’adatu Soja ta bayyana matuƙar alhininta bisa faruwar lamarin, inda ta ce wajibi ne jami’an tsaro su gudanar da bincike mai zurfi domin gano haƙiƙanin abin da ya faru, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin rikicin.
Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Shugabar ta jaddada cewa majalisar ƙaramar hukumar Tudun Wada za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A nasa ɓangaren, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa bayan kammala taron rabon tallafin kayan Azumi da na Sallah ga al’ummar yankin a ranar 13 ga Maris, 2026, ya samu rahoton cewa wasu bata-gari sun yi yunƙurin tayar da tarzoma a wurin.
Doguwa ya ce rikicin ya yi sanadin rasuwar wani jami’in tsaro na Civil Defence, inda ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga hukumar, iyalan mamacin da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Tudun Wada baki ɗaya.
Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano waɗanda suka haddasa tashin hankalin tare da ɗaukar matakin doka a kansu.
Haka kuma, ya gargaɗi masu yaɗa labaran ƙarya da kalaman ɓatanci da ke alaƙanta shi da lamarin, yana mai cewa zai ɗauki matakan doka domin kare mutuncinsa da na al’ummar da yake wakilta.
Da yake ƙarin bayani kan lamarin, mai magana da yawun hukumar Civil Defence reshen jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya ce jami’in da ya rasa ransa ma’aikacin sa-kai ne, ba na dindindin ba.
Ya ƙara da cewa sun tuntuɓi sashen hukumar na ƙaramar hukumar Tudun Wada domin samun ƙarin bayani kan musabbabin mutuwar, sannan daga nan za su bayyana matakin da za su ɗauka.






