Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano (PHIMA) ta gudanar da ziyarar bincike kafin rijista a wasu cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu, domin tabbatar da cewa sun cika ƙa’idojin aiki da ake bukata kafin fara gudanar da ayyukansu.
Binciken na daga cikin aikin sa ido da hukumar ke yi kan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu, domin tabbatar da cewa suna bin dokoki da ƙa’idojin da gwamnati ta shimfiɗa, tare da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar PHIMA, Fauziyya Habib Mahmud, ta rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce tawagar binciken ta kasance ƙarƙashin jagorancin Daraktan Sashen Kiwon Lafiya da Ayyukan Jinya na hukumar, Dakta Sulaiman Ibrahim, wanda ya jaddada muhimmancin bin dokoki da ka’idojin da suka shafi harkar kiwon lafiya.
A yayin ziyarar, tawagar ta kai duba zuwa Afrimedisc Minimally Invasive Surgery Hospital, domin tantance yadda asibitin ya shirya da kuma yadda yake bin ƙa’idojin da ake buƙata ga cibiyoyin lafiya masu zaman kansu.
Tawagar ta lura cewa asibitin na da ɗakuna 18 tare da gadaje 22, kuma an tsara shi yadda ya dace tare da kayan aikin likitanci na zamani da ake buƙata domin gudanar da tiyata ta zamani (minimally invasive surgery).
Har ila yau, tawagar ta bayyana cewa asibitin na da shirin samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga marasa lafiya.
Sai dai tawagar ta lura da buƙatar samar da banɗaki a wurin zaman ma’aikatan jinya (Nurses Station) domin ƙara sauƙaƙa aiki da inganta yanayin aiki ga ma’aikatan jinya. “Mai asibitin ya amince da shawarar tare da ba da tabbacin cewa za a samar da wannan gini cikin gaggawa,” in ji sanarwar.
Da yake jawabi yayin binciken, jagoran tawagar, Dakta Sulaiman Ibrahim, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu sun cika mafi karancin ƙa’idojin da ake buƙata domin samar da lafiya mai inganci da tsaro ga al’umma.
Ya ƙara da cewa hukumar PHIMA na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa dukkan asibitoci masu zaman kansu suna gudanar da ayyukansu bisa dokoki da ƙa’idojin da aka amince da su domin kare lafiyar marasa lafiya da walwalar al’umma.
A yayin wannan aiki kuma, hukumar ta rufe wasu cibiyoyin lafiya da aka samu suna aiki ba tare da bin ƙa’idojin da aka gindaya ba, a wani mataki na tabbatar da bin doka da kare lafiyar jama’a.
Hukumar ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu suna aiki ne bisa ƙa’idoji da dokokin da aka amince da su domin kare lafiya da jin daɗin al’umma.






