Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Kano, Amb. Munzali Danbazau, ya jagoranci rabon tallafin kuɗin jari na shirin Abba Gida-Gida ga mata daga mazaɓun ƙaramar hukumar.
Da yake jawabi yayin rabon tallafin a ofishin Hisba na yankin, Danbazau ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa abin da ya kira “kaɓakin arziƙi” da ya sauke wa mata a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar, ciki har da Birnin Kano.
“Abba ya cika g
Gwarzo. Duk abin da ake buƙata yana yi. Muna gode wa Mai Girma Gwamnan Kano bisa wannan tallafi da ya bai wa mata. Haƙiƙa al’umma na cikin farin ciki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a matsayinsu na shugabannin jam’iyya a matakin ƙaramar hukuma, suna gode wa gwamnatin jihar bisa ƙoƙarin da take yi na tallafa wa al’umma, tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da ba gwamnan ikon tafiyar da mulki cikin nasara.
Danbazau ya bayyana cewa rabon tallafin na tafiya cikin tsari, yana mai cewa za a ci gaba da gudanar da shirin har sai dukkan matan da aka tsara sun amfana.
Ya kuma buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata domin fara sana’o’in dogaro da kai da za su taimaki kansu da iyalansu.
Ya yi fatan matan za su ci gaba da yi wa Gwamnan addu’a domin samun nasara a jagorancinsa.
An gudanar da rabon tallafin ne ƙarƙashin kulawar shugaban CRC na ƙaramar hukumar Birnin Kano, Alhaji Labaran Shamba.
Sai dai a yayin rabon, wasu daga cikin matan sun koka cewa an gayyace su ne bayan an riga an tattara sunayensu tun farko, amma ba su samu tallafin ba.
Da aka nemi jin ta bakin shugaban CRC na Birnin Kano, ya ƙi yin magana kan batun.
Sai dai wani daga cikin tawagar da ke kula da tsarin rabon ya ce an samu kuskure ne, wanda za a gyara domin tabbatar da cewa kowa ya samu tallafinsa.






