Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Gwamnatin jihar Kano ta hannun Ma’aikatar Jin Ƙai da Rage Talauci ta kai tallafi ga al’ummar da gobara ta shafa a garin Zago da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Al’umma na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi, ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce an raba tallafin kuɗaɗe har Naira miliyan shida da dubu ɗari biyar da saba’in da shida da ɗari biyar da talatin da bakwai da ɗigo talatin da uku (N6,576,537.33) ga iyalai 28 da gobarar da ta tashi a watan Fabrairun 2025 ta shafa.
Da take jawabi yayin rabon tallafin, Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Amina Yusuf ‘Yargaya, ta ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf tana damuwa matuƙa da duk wata matsala da ta shafi rayuwar al’umma, musamman waɗanda suka fuskanci bala’i.
Ta ƙara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da tallafa wa al’umma a duk lokacin da irin wannan ƙalubale ya taso domin tabbatar da jin daɗi da walwalar jama’a.
Haka kuma ta buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da abin da suka samu ta hanyar da ta dace.
Shi ma da yake jawabi, Sakataren Zartarwa na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Abdullahi Isyaku Kubarachi, ya bayyana cewa an gudanar da bincike domin tantance girman asarar da gobarar ta jawo kafin a samar da tallafin.
Ya kuma roƙi al’umma da su riƙa kula da yadda suke amfani da wuta, musamman a gidajensu, tare da tabbatar da kashe wuta bayan kammala ayyukan gida kafin kwanciya barci.
A nasa ɓangaren, Mashawarcin Gwamna na Musamman kan Ayyukan Jin Ƙai, Dakta Garba Ibrahim, ya buƙaci al’umma da su riƙa yin taka-tsantsan domin kaucewa aukuwar gobara, yana mai jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da taimaka wa duk wanda bala’i ya shafa.
Shi kuma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan jihar Kano kan Tallafin Al’umma, Muttaƙa Sani Gaya, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da walwalar al’umma, musamman masu rauni da waɗanda bala’i ya shafa.
Da yake bayyana godiyarsa, shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta, Jamilu Abubakar Ɗanbatta, wanda Abdulƙadir Muhammad ya wakilta, ya gode wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan tallafi, yana mai cewa taimakon zai rage wa waɗanda abin ya shafa radadin asarar da suka yi.
Waɗanda suka amfana da tallafin sun nuna godiyarsu ga gwamnatin jihar Kano bisa tallafin da aka kawo musu a lokacin da suka fi buƙata.






