Taro Tsakanin Masu Maganin Gargajiya Da Likitocin Zamani Zai Kawo Fahimtar Juna -Dakta Yakub Maigida Kachako

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana taron bita da aka gudanar ƙarƙashin Hukumar PHIMA tare da masu maganin gargajiya a matsayin wani muhimmin mataki na inganta fahimtar juna tsakanin masu maganin gargajiya da likitocin zamani.

Ɗaya daga cikin fitattun masu maganin gargajiya a Kano, Dakta Yakub Maigida Kachako ne ya bayyana haka, inda ya ce rashin irin wannan mu’amala a baya ne ya haifar da saɓanin fahimta da kuma rashin haɗin kai tsakanin bangarorin biyu.

Ya ƙara da cewa irin wannan haɗuwa na taimaka musu a matsayinsu na masu maganin gargajiya wajen karɓar shawarwari da saƙonni kan yadda za su inganta ayyukansu.

Ya ce idan babu irin wannan mu’amala, sai a riƙa jin gargaɗi kawai ba tare da cikakken bayani ba, wanda kan sa wasu su ɗauka ana yunƙurin hana amfani da maganin gargajiya ne saboda rashin fahimta.

Dakta Kachako ya yi nuni da cewa taron zai taimaka wajen fayyace dokoki da ƙa’idojin aiki, da sanin abin da ɓangarorin ke so ko ba sa so, domin kowa ya san iyakarsa da yadda zai gudanar da aikinsa cikin mutunta juna.

Ya kuma bayyana cewa bai dace a riƙa ƙin amincewa da maganin gargajiya gaba ɗaya ba, musamman ganin cewa rahotannin World Health Organization sun nuna cewa kusan kashi 80 cikin 100 na al’ummar duniya na dogaro da maganin gargajiya wajen kula da lafiyarsu.

A cewarsa, abin da ya fi dacewa shi ne a riƙa amfani da maganin gargajiya ta hanyar da ta dace, tare da wayar da kan jama’a kan inda ya kamata su nemi magani da kuma yadda za su yi amfani da shi cikin aminci.

Ya bayyana cewa taron ya ƙunshi faɗakarwa kan cutar Lassa da kuma ilimin aikin ungozoma, inda aka tattauna hanyoyin kariya da yadda za a gane alamomin cutar.

Dakta Kachako ya ce a fahimtarsu ta gargajiya, cutar Lassa zazzaɓi ne mai tsanani da aka fara gano shi a Najeriya a shekarar 1996 a jihar Borno, kuma an sanya masa suna ne daga garin Lassa inda aka fara gano ɓullarsa.

Ya ƙara da cewa ko da yake suna iya fahimtar wasu alamomi ta hanyar ɗabi’ar cutar, ba sa tsoma baki a kula da irin wannan zazzabi mai haɗari; idan suka ci karo da wanda ake zargin ya kamu, sukan tura shi asibiti domin samun kulawar ƙwararrun likitoci.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani