PHIMA da KHEFUND Sun Yi Taron Bita Ga Masu Maganin Gargajiya Kan Kariyar Cututtuka Masu Yaɗuwa

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf na ci gaba da ƙoƙarin inganta harkokin kula da lafiya a matakin farko, la’akari da muhimmiyar rawar da masu maganin gargajiya ke takawa wajen kula da lafiyar al’umma, kasancewar su ne mafi kusa da jama’a.

A wannan dalili ne Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko tare da Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu (PHIMA) da haɗin gwiwar gidauniyar tallafawa lafiya ta KHEFUND suka shirya taron bita na yini guda ga shugabannin masu maganin gargajiya daga sassan jihar domin wayar da su kai kan hanyoyin kariya daga cututtuka masu yaɗuwa.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kano, Farfesa Salisu Ahmad, ya bayyana hakan yayin buɗe taron da aka gudanar a ranar Talata, inda ya ce akwai tsare-tsare na ci gaba da horas da masu maganin gargajiya domin ƙara inganta ayyukansu da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninsu da likitocin zamani.

Ya ƙara da cewa taron ƙarawa juna sani abu ne mai matuƙar muhimmanci domin tattauna sabbin cututtuka da hanyoyin yaɗuwarsu, musamman ganin cewa cututtuka na iya yaɗuwa ta hanyoyi daban-daban ciki har da ta numfashi, don haka akwai buƙatar kowa ya ɗauki matakan kariya.

Farfesa Salisu Ahmad ya ce galibi masu maganin gargajiya sune farkon waɗanda marasa lafiya ke zuwa wurinsu, saboda haka wajibi ne su san yadda za su kare kansu daga kamuwa da cututtuka yayin da suke ba da taimako.

Ya kuma buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu tare da yaɗa shi ga abokan aikinsu domin a samu fahimta a tsakanin al’umma, wanda hakan zai taimaka wajen daƙile yaɗuwar cututtuka.

A nata jawabin, shugabar riƙo ta Hukumar PHIMA, kuma Daraktar Mulki, Hajiya Khadija Hussain Sa’id, ta bayyana cewa an shirya taron ne saboda yadda ake samun ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa, inda ta ce sau da yawa marasa lafiya kan fara zuwa wurin masu maganin gargajiya kafin zuwa asibiti.

Ta yi gargaɗin cewa wasu cututtuka kan bayyana da alamomi irin na mura ko tari, amma a haƙiƙanin gaskiya suna iya zama cututtuka masu tsanani kamar mashaƙo ko wasu cututtuka masu haɗari, wanda hakan na buƙatar kulawa ta musamman.

Ta shawarci masu maganin gargajiya da su riƙa amfani da kayan kariya kamar takunkumi da safar hannu kafin su taɓa marasa lafiya domin kare kansu, tare da tura duk wani lamari da suka kasa gane shi zuwa asibiti domin a gudanar da gwaje-gwaje.

Hajiya Khadija ta ƙara da cewa akwai cibiyoyi da ofisoshin kula da cututtuka masu yaɗuwa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, kuma za a bai wa mahalarta lambobin tuntuɓa domin sanar da hukumomi cikin gaggawa idan sun lura da wata alama ta ɓarkewar cuta.

Ta bayyana jin daɗinta da yadda masu maganin gargajiya da sarakunansu suka amsa gayyata, tare da jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren gargajiya da na zamani zai taimaka wajen samar da al’umma mai koshin lafiya.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken “Wayar da Kai Kan Cututtuka Masu Yaɗuwa a Cikin Al’umma”, inda gwamnatin jihar Kano ta bai wa PHIMA damar shirya shi tare da hadin gwiwar gidauniyar KHEFUND domin kara wayar da kan masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani