Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Lawan Ɓatagarawa, ya jaddada muhimmancin haɗa kai tsakanin gwamnati da kowane ɓangare na al’umma domin magance matsalar tsaro a ƙasar nan.

Ɓatagarawa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a taron da Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu ta Arewa (Grain Marketers Association of Northern Nigeria) reshen Jihar Kano ta shirya, wanda aka gudanar a Gidan Mumbayya, domin tattauna manyan matsalolin da ke addabar ƙasa.

Ya yaba da shirya taron, yana mai cewa ba daidai ba ne a ɗora dukkan alhakin warware matsalolin ƙasa, musamman ta tsaro, a kan ‘yan siyasa kaɗai.

A cewarsa, sai an haɗa kai da dukkan sassan al’umma kafin a samu mafita mai ɗorewa.

“Al’amarin tsaro yana da tushe. Idan ba a gyara tushen yau da gobe ba, matsalar za ta ci gaba da rikicewa. Tattaunawa da kowa ya zo da irin nasa ra’ayi abu ne mai muhimmanci. Duk da cewa hukumomi a kowane mataki sune ke da babban nauyi, amma kowane ɗan ƙasa na da haƙƙin bai wa gwamnati goyon baya. Sai dai a halin da ake ciki, gwamnati ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro a ƙasar nan,” in ji Ɓatagarawa.

Ya yi nuni da yadda a ‘yan kwanakin nan aka samu kisan gilla a jihohin Kwara, Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Neja, inda ya ce irin waɗannan hare-hare sun zama ruwan dare, ana kai wa ƙauyuka hari, ana tauye mutuncin maza da mata a gaban ‘ya’yansu, alhali cikakken alhakin tsaro yana hannun gwamnati.

Ɓatagarawa ya ƙara da cewa inganta tsaro ya haɗa da hana riƙe makamai ga waɗanda doka ba ta amince da su ba, tare da karɓe makaman da ke hannun masu laifi.

Ya kuma soki batun sulhu da ‘yan bindiga, yana cewa: “Maganar sulhu da wanda ke da makami, alhali ɗayan ba shi da shi, ba sulhu ba ne, mika wuya ce kawai.”

Ya jaddada cewa dole ne a ɗauki matakai masu ƙarfi na inganta tsaro, tare da duba tsarin tattalin arziƙi, musamman yadda yawan jama’a ke ƙaruwa ba tare da tattalin arziƙin ƙasa yana ƙaruwa yadda ya dace ba.

A cewarsa, samar da ayyukan yi, sana’o’i da kasuwanci da za su tallafa wa rayuwar jama’a zai taimaka matuƙa wajen rage matsalar tsaro, domin “wanda bai ci abinci ba, ba zai iya tunanin zaman lafiya ba.”

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Masu Samar da Abinci a Buhu ta Arewacin Nijeriya, reshen Jihar Kano, Alhaji Umar Abba Mustapha Ungogo, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin bunƙasa tattalin arziƙi da zaburar da matasa, musamman duba da halin da yankin Arewa ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki da barazanar tsaro.

Ya ce sun lura da cewa a Arewa mutane da dama na jiran wasu su yi aiki, sannan a ɗora musu laifi idan abu ya lalace. “Mun yi barci muna zargin ‘yan siyasa da masu ilimin boko. Lokaci ya yi da kowa zai tashi ya ba da gudunmawa a inda ya dace, domin ceto makomar Arewa,” in ji shi.

Ungogo ya ƙara da cewa rashin ayyukan yi ya jefa matasa cikin shan miyagun ƙwayoyi da aikata munanan laifuka.

Ya ce da a ce an kafa kamfanoni masu aiki, da dubban matasa sun samu aikin yi, da kuma rage yawaitar miyagun laifuka.

Ya bayyana cewa taron ya shafi kowa da kowa—malamai, masana, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da sauran al’umma—inda ya yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su yi amfani da sauƙin farashin kayan abinci da Allah Ya kawo, ta hanyar tallafa wa manoma, musamman wajen rage tsadar taki da sauran kayan noma.

Ya jaddada cewa saukar farashin kayan abinci ya sa manoma da dama ba su ci riba ba saboda tsadar kayan aikin noma. Don haka ya bukaci gwamnati da ta rage farashin taki da sauran kayan noma, domin ƙarfafa manoma su yi noman damina mai zuwa, yana mai gargadin cewa idan aka gaza yin noma, ana hasashen tsadar kayan abinci za ta ƙara tsananta nan gaba.

A nata jawabin, Hajiya Sayyida Sani Rogo, ‘yar kasuwa, kuma ‘yar siyasa, shugabar Makarantar Islamiyya ta Idrisiyya da ke Hotoron Arewa, ta bayyana farin cikinta da halartar taron, tana mai jaddada rawar da ‘yan kasuwar buhu ke takawa wajen wadatar da al’umma da abinci.

Ta ce ‘yan kasuwar buhu sune ke sayo kayan abinci daga manyan kasuwanni kamar Dawanau da Singa, su rarraba su zuwa unguwanni da ƙauyuka.

Ta ƙara da cewa idan ba don ƙoƙarin ‘yan kasuwa ba, da samun abinci ya yi matuƙar wahala.

Hajiya Sayyida ta bayar da misali da cewa a kusan watanni takwas da suka gabata, ta yi kwangilar fitar da waken suya da zobo daga Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya, inda aka sayo kayan daga kasuwar Dawanau, aka shirya su cikin kwantena, aka kai su tashar jiragen ruwa ta Ikko, daga nan zuwa Saudiyya.

Ta ce hakan shaida ce cewa ba a Kano ko Nijeriya kaɗai ake kai kayan abinci ba, har ma ana fitar da su ƙasashen waje.

Taron ya samu halartar mutane da dama, ciki har da Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu ta Arewa, Alhaji Mustapha Sudawa, da sauran ‘yan kasuwa daga ciki da wajen Kano, tare da malamai na jami’a da na addini.

Daga cikin masu gabatar da jawabi akwai Dakta Dukawa.
Haka kuma, an samu bayar da tallafi a yayin taron, inda Alhaji Muhammad Adakawa, Hajiya Sayyida Sani Rogo da Alhaji Lawan Mai Masara suka bayar da gudunmawar Naira 50,000 kowannensu, tare da sauran gudunmawar da aka karɓa daga mutane da dama.

  • Related Posts

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Asibitin Ƙashi na Tarayya da ke Dala, Kano, ya ba wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi, Hon. Abba Kabir Bichi, lambar karramawa bisa gudunmawa…

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gidauniyar NNPCL, reshen ayyukan jin ƙai na NNPC Ltd, ta ƙaddamar da sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani mai ƙarfin 1.5 Tesla MRI Scan da aka…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity