2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu bai samu wakilci na gari a Majalisar Dattawa ba.

Ya ce kowanne Sanata da ya zo ya tafi, har zuwa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya wanda shi yafi kowa dadewa yayi shekaru 16 a matsayin Sanatan yankin, amma babu wani aiki na cigaba da al’ummar Kano ta Kudu za su yi alfahari da shi kawo.

Abba Umar Tiga ya ce, saboda haka ne a shekarar 2023 suka hadu suka sauya shi, suka kawo Sanata Kawu Sumaila da kyakkyawan zato a kansa, amma abin da ake tsammani ba haka aka gani ba.

“Duk mai son cigaban Kano ta Kudu a wannan karo na zaben 2027, dole ne mu hade kanmu waje daya mu tsaya mu sauya wakilci domin samun kyakkyawar wakilci da zai amfanar da dukkan al’ummar yankin,” in ji shi.

Ya kara da cewa yankin Kano ta Kudu na fama da dimbin kalubale duk da kasancewarsa yanki mafi yawan mazabu a duk fadin kasar nan. A cewarsa, da ace ana bin tsarin yawan mazabu ne wajen zaben Shugaban Majalisar Dattawa, to daga yankin ne ya kamata a rika samu, amma sai gashi manyan matsaloli na damun yankin kuma basa amfanar abin da ya kamata.


Abba Umar Tiga ya yi kira ga al’ummar Kano ta Kudu su fito su yi aiki tukuru domin kawo sauyi domin suna da kyakkyawan fata akan Dakta Alkasim Ibrahim Batayya idan ya zama sanata , saboda irin ayyukan alheri da yake yi a baya da kuma yanzu, duk da cewa baya rike da wani mukami na siyasa.

A cewarsa, Dakta Batayya kamar likita ne da ya san ciwo ya kuma san maganin da zai rubuta domin samun waraka. Idan al’ummar Kano ta Kudu suka zabe shi a matsayin Sanata a zaben 2027 karkashin jam’iyyar NDC, tabbas za su samu mafita, domin zai hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki masu kishin cigaban yankin domin fitar da Kano ta Kudu daga matsalolin da ke damunta.

  • Related Posts

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazaɓar Gwale a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Hon. Abdulhadi Dalhatu Awilo, ya bayyana cewa shi ne halastaccen ɗan takarar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength