Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027 na kananan hukumomi 44 na jihar.

Galadima ya bayyana hakan ne bayan zaman gyare-gyaren da aka gudanar a ma’aikatar, inda ya yabawa dukkan shugabannin kananan hukumomi, daraktocin mulki, daraktocin kudi da ma’aji, da kuma shugabannin sassa bisa hadin kan da suka nuna.

Ya ce, an shigar da dukkan dokoki da ka’idojin da Gwamnatin jihar Kano ta bayar domin tabbatar da kasafin kudin na 2027 ba tare da wata matsala ba, domin gudun samun gibi a ayyukan raya karkara da aka tsara wa al’umma.

Ya kara da cewa, kasafin kudi hasashe ne ba kudi a kasa ba, hasashe ne na abin da ake sa ran kananan hukumomi za su tara a matsayin kudaden shiga, domin hada kai wajen aiwatar da ayyuka na yau da kullum da kuma ayyukan da al’umma za su amfana.

Daga karshe, a madadin Mai Girma Gwamnan jihar Kano, Injinaiya. Abba Kabir Yusuf,.Hon.Bashir Abubakar Galadima ya yi kira ga kananan hukumomi 44 da su kara zage damtse wajen tara kudaden shiga fiye da yadda suke yi a baya. Ya jaddada cewa shigar kudaden shiga cikin asusun baitulmalin kananan hukumomin ne zai ba su fifiko da kuma damar samun karin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazaɓar Gwale a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Hon. Abdulhadi Dalhatu Awilo, ya bayyana cewa shi ne halastaccen ɗan takarar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength