Daga Ibrahim Muhammad
Ƙananan ‘yan kasuwar da ke gudanar da harkokinsu a Dandalin Fagge suna cikin fargabar tashinsu daga wajen da suke gudanar da kasuwancinsu da ƙaramar hukumar Fagge take shirin yi.
Sun bayyana cewa yawanci suna fargabar makomarsu idan aka tashe su, kasancewar sun shafe tsawon shekaru a wajen suna sana’o’i, wasu na fawa, wasu kuma suna sayar da kayan masarufi ga al’ummar ƙwaryar Fagge.
‘Yan kasuwar sun koka da cewa ƙaramar hukumar ta Fagge ƙarƙashin jagorancin Hon. Salisu Usman Masu za ta tashi ɓangaren da mahauta da sauran masu sana’o’i suke ne domin haɗe su a waje ɗaya da sauran masu saye da sayarwa a ɓangaren da masu kayan miya suke, matakin da suke ganin zai jawo ƙara cinkushe kasuwar.
Wani bincike da muka gudanar ya nuna mahukuntan ƙaramar hukumar ta Fagge za su tashi ɓangaren kasuwar Dandalin ne, don haɗe su waje guda sakamakon yadda ɓangaren da za a tasa ya zama wani waje da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ke hada-hada a wajen lamarin da ka iya gurɓata tarbiyya da barazana ga tsaro.
Ƙaramar hukumar ta Fagge ƙarƙashin jagorancin.Hon. Salisu Usman Masu za ta yi amfani da filin ne, wajen gina makaranta da kuma ofishin haɗakar jami’an tsaro domin hana ɓata-gari yin sansani a wurin suna hada-hadar miyagun ƙwayoyi.
Domin tabbatar da gaskiyar dalilin tashin ‘yan kasuwar da haɗe su waje ɗaya da suka ce za a yi da hakan zai ƙuntata masu, Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Salisu Usman Masu, amma haƙar sa ba ta cimma ruwa ba.
Mun aika masa da saƙon kar-ta-kwana da har zuwa rubuta wannan labarin bai ce komai ba.
‘Yan kasuwar na Dandalin sun bayyana cewa suna goyon bayan matakin kawar da ɓata-gari da ke yin sansani a kasuwar suna sayar da miyagun ƙwayoyin dama hakan na damunsu.
“Don haka, roƙon da muke yi wa shugaban ƙaramar hukuma Hon. Salisu Usman Masu kasancewar mun shiga fargabar tashin namu da aka ce za a yi har wasunmu da dama sun rasa jarinsu a matsayinsu na masu ƙaramin ƙarfi, muna fata za a kawo mana ɗaukin tallafa mana da jari,” in ji su.






