Ƙungiyar Lauyoyi Ungogo Kano Sun Yaba Wa Gwamnatin Kano Kan Kafa Kwamiti Don Binciken Kwamishina Da Ake Zargi Da Belin Dilan Miyagun Ƙwayoyi

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), reshen Ungogo jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Ahmad Abubakar Gwadabe ya yaba da gode wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf kan ɗaukar mataki na gaggawa da kafa kwamitin bincike domin duba zargin da ake yi cewa wani jami’in gwamnati bisa tsayawa karɓar belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da ke fuskantar shari’a a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da ƙungiyar ta fitar ga manema labarai da ke da sa hannun shugaban ta Batista Ahmad Abubakar Gwadabe.

Ƙungiyar lauyoyin reshen Ungogo ta kalli lamari da matuƙar damuwa, kasancewar laifukan da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi suna da nasaba da hauhawar matsalolin tsaro, taɓarɓarewar tarbiyyar matasa da kuma yawaitar munanan ɗabi’u a cikin al’umma.

Laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi na jawo haifar da tashin hankali, barazana ga tsaro daga zaman lafiyar al’umma da lalata ginshiƙin kyawawan ɗabi’u.

Sun bayyana cewa duk suna yabawa da kafa kwamitin bincike, suna kuma kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da cewa rahoton kwamitin ya kasance a bayyane don tabbatar da gaskiya da riƙon amana, suna kuma buƙatar mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da adalci da rashin son zuciya duk da cewa ba a bayyanawa jama’a sharuɗɗan aikinsu ba.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe shugaban lauyoyin ya ce reshen Ungogo na nan daram wajen tsayawa don ganin adalci, gaskiya a cikin mulki, da kuma kare muradun al’umma za su cigaba da mara baya ga dukkan wani yunƙuri da ke neman kare doka da oda da kuma kare jihar Kano daga mummunan tasirin shan miyagun ƙwayoyi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo