A wani taro mai cike da alhini da juyayi da aka gudanar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 a muhallin Jannatu Darur Rahma dake Dembo a Zariya, Harkar Musulunci a ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta gudanar da taron tunawa da cika shekaru 11 da kisan gillar da aka yi wa membobinta 34 a Zariya a yayin wani zanga-zangar lumana ta ranar Qudus a shekarar 2014.
Taron ya kasance cike da jimami da alhini tare da karramawa ga waɗanda suka rasa rayukansu, kazalika an sake jaddada kiran neman adalci.
Sannan, Harkar Musuluncin ta bayyana goyon bayanta na dindindin ga al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, tana mai cewa ƙudurinta na tsaya musu tsayin daka bai sauya ba, kuma ba zai taɓa gushewa ba.
A yayin ganawarsa da manema labarai a yayin taron, Sayyid Badamasi Yaqoub, ɗan uwa ga jagoran Harkar Musulunci, ya jaddada cewa; “Wannan gwagwarmaya da muke yi ta neman adalci, dama ta gaji kule daga mahukunta; “Dama ita wannan hanya, ita ke nan ba ta da canji. Hanya ce ta kira zuwa ga addinin Allah, tabbas akwai mutuwa a cikinta.”
Ya ci gaba da cewa; “Wannan abin da Annabawa suka sha gwagwarmaya a kai ke nan. Saboda haka da zarar ka ce Allah da ma’anarsa, to za ka haɗu da fushin waɗanda ba su yarda da wannan ba. Suna ganin su mulkinsu kake ƙalubalanta, saboda haka lallai ba za su barka ba”, in ji shi.
Sai dai ya ce waɗanda aka kashe ba su yi laifin komai ba, illa kawai; “sun ce Ubangijinsu Allah ne, ba su yarda da zalunci ba, suka tsaya a kai”.
Dangane da matakin da za su ɗauka kuwa, Shaikh Badamasi ya tabbatar da cewa su dai za su ci gaba da gwagwarmayarsu, kuma da wannan gwagwarmayar ne ƙarshen zalunci zai zo, kamar yadda ya ce; “Da wannan gwagwarmayar ne ƙarshen zalunci zai zo. Ta wannan yunkurin da suke yi na kisa, ta wannan hanyar ce ƙarshen su zai zo”.
Ya jaddada cewa suna alfahari da waɗanda aka kashe, kuma ba za su taɓa mantawa da su ba. Inda ya jaddada aniyar cewa, wannan ba zai sanyaya musu guiwa ba, za su ci gaba da kasancewa da al’ummar Falasdinu; “Waɗannan yara an shahadantar da su ne a kan Qudus. Yanzu al’ummar Musulmi su dubi abin da yake faruwa a Gaza. Yanzu mutum ba zai iya kallon abin da yake faruwa a Gaza ba, duk magoya bayansu a kewaye da su, duk ƙasashen Musulmi ne. Ita kanta Isra’ila an kafa ta a ƙasar Musulmi ne, Masar Musulmi ne, amma kuma sun kewaye sun hana a shiga da abinci, Jordan Musulmi ne, sun kewaye sun hana abinci; kullum ana mutuwa da yunwa, ba abinci, ba ruwa, ba komai. Suna bin goyon bayan waɗannan azzaluman mahukunta”.
Ya ƙara da cewa; “Wannan zaluncin da ake yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, muna nan tare da su, kuma Wallahi Summa Tallahi, da za mu samu dama, za mu je Gaza mu bayar da jininmu a kan su”, ya jaddada.
Malam Ibrahim Abubakar, ɗaya daga cikin masu shirya wannan taron, ya tabbatar da cewa suna tuna wannan kisan gilla a duk ranar 25 ga watan Yulin kowacce shekara; “A wannan rana ta 2014 sojojin Nijeriya suka kashe mana mutum 34, suka raunata aƙalla 80; masu ƙaramin’ da manyan raunuka. Duk a irin wannan rana idan ta zagayo duk shekara muna haɗuwa a wannan muhallin mu yi musu addu’o’i da saukar Alƙur’ani. Sannan mu yi taruka da jawabai na tuna su”.
Ya ce duk wanda ya tsayawa gaskiya zai fuskaci irin wannan. Ya ce a duk inda kake dole a ci gaba da neman haƙƙin al’ummar Falasdinu.
Tunda farko an soma taron da addu’o’i da karatun Alƙur’ani mai girma, tare da gabatar da fareti da kuma jawabai daga Malamai.
Maryam Ɗalhatu, ɗaya ce daga cikin ‘yan’uwan waɗanda aka kashe a wannan rana, ta ce; ta yi farin ciki cewa ana tunawa da su a kowacce shekara, sai dai har yanzu tana kukan rashin su.
Sai dai ta ce; “Saƙona ga azzalumai shi ne, wannan hanyar da suka ɗauka ta kashe mutane, ba hanya ce mai ɓullowa ba, su sani cewa wannan abin da suke yi ba zai kai su ga ko’ina ba sai asara, tun daga duniya har lahira”, in ji ta.
Kazalika, Alƙasim Muhammad Gyallesu, ɗaya daga cikin waɗanda aka raunata a wannan rana, shekaru 11 da suka gabata, amma har yanzu illar harbin da aka yi masa na ci gaba da nunawa.
“Ina cikin waɗanda sojoji suka harba a lokacin. Ba mu ɗauke da komai a hannunmu a lokacin, illa iyaka kawai mun fito domin jajen mu da nuna goyon baya tare da Allah-wadai da zaluncin da ake yi wa al’ummar Falasdinu.






