Daga Hadi Bawa
A jawaban da aka gabatar a taron kwanaki biyu da Gidauniyar Sardauna ta shirya a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna don yi nazari kan kamun ludayin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, sun buƙaci ‘yan Arewa da ke son kujerar shugaban ƙasa a 2027 su jira zuwa 2031.
A jawabinsa a taron, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu, ya tabbatar wa taron cewa, bisa ƙa’idar karɓa-karɓa da ake a kai, sai 2031 yankin Arewa zai amsa.
Ya ce, “A shekarar 1999, ’yan Arewa masu kishin ƙasa irin su Solomon Lar, Adamu Ciroma, Abubakar Rimi, da Jerry Gana, sun amince cewa, karɓa-kaɓa a mulki shi ne jigon zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. Duk da wannan yarjejeniyar ba a rubuce take ba, amma Arewa za ta sake cancantar samun damar hawa kujerar shugaban ƙasa ne a 2031,” in ji shi.
Ya bai wa ‘yan Arewa hakuri da cewa, “Mu yi haƙuri, Nijeriya ba za ta gushe ba kafin 2031. Idan lokacinmu ya yi, al’umma za ta sani.”
Shi ma a jawabinsa a taron, Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce, yankin Arewa zai mara wa shugaba Bola Tinubu a fafutukarsa ta neman tsayawa zaɓe a 2027.
Ya ce goyon baya da aka bai wa Tinubu a zaɓen 2023 ya fara haifar da ɗa mai ido a ɓangarorin ayyukan more rayuwa da tsaro da noma da kuma makamashi.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya yi gargaɗi kan hatsarin da ke ƙunshe cikin hana ‘yan takarar Arewa tsayawa zabe a 2027.
Johnson ya ce idan har APC da Tinubu za su iya karyawa da kawo ƙarshen tsarin da aka jima a kai na siyasa da addini suka ɓullo da ‘Muslim-Muslim Ticket’ a 2023, babu wani dalili na tsayar da ɗan takarar Kudu kaɗai.
Ya ce, “A baya muna kan tsari ko al’adar haɗa Musulmi da Kirista ko Kirista da Musulmi, da kuma juyawa daga Arewa zuwa Kudu ko daga Kudu zuwa Arewa.
“Amma a zaɓen da ya gabata, an yi watsi da batun haɗa tikitin Musulmi da Kirista. Aka yi tikitin takara tsakanin Musulmi da Musulmi, kuma ƙasar nan ba ta ruguje ba, don me wani zai yi tunanin ƙasar za ta rushe idan ɗan takarar Arewa ya ci zaɓe a 2027?”
Shi ma Kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce: “A shekara ta 2027, ‘yan Nijeriya za su kaɗa ƙuri’a su kori APC saboda sun gaza. Ba za su kasance a kan karaga ba bayan 2031.”
Sai dai a hirarsa da jaridar PUNCH, Sakataren Yaɗa Labarai na APGA na ƙasa, Ejimofor Opara, ya ce jam’iyyar za ta ba yankin Kudu fifiko idan lokacin zaɓen shugaban ƙasa ya yi.
Ya ce, “Yanzu lokacin yankin Kudu ne don samar da shugaban ƙasa a 2027. Tabbas za mu tallata ɗan takarar Kudu.”
Shi dai wannan taron, wanda aka kira shi bayan wasu kalamai na nuna gazawa wajen kula da yankin Arewa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnatin Tinubu, ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a siyasar yankin Arewa.






