Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An tabbatar da rasuwar ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu da ke wakiltar ƙananan hukumomin Ungoggo da Birnin Kano.
Marigayan sun haɗa da Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungoggo, da kuma Hon. Sarki Aliyu Daneji, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Malam Kamaludeen Sani Shawai, ne ya tabbatar da rasuwar Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo a yammacin ranar Laraba, yayin wata tattaunawa da manema labarai.
A cewarsa, marigayin ya kamu da rashin lafiya ne jim kaɗan da isa Majalisar a safiyar ranar Laraba, inda nan take aka garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci. Sai dai daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Shi ma ɗan Majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano, Hon. Sarki Aliyu Daneji, ya rasu bayan rasuwar ɗan majalisar Ungoggo, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Hon. Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar.
Tuni aka gudanar da jana’izar marigayi Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, yayin da za a gudanar da jana’izar marigayi Hon. Sarki Aliyu Daneji a safiyar Alhamis ɗin nan.






