Jami’an Tsaro Na Ci Mana Zarafi A Kan Hanyoyi -Shugaban RTEAN Reshen Kasuwar Singa, Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban Kungiyar Direbobi ta RTEAN, reshen Kasuwar Singa a Kano, Kwamared Yakub Haruna, karkashin jagorancin Alhaji Baba Mai Duniya, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen gyara manyan hanyoyin da ake zirga-zirga a faɗin ƙasar nan.

Yakub Haruna ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Kano, inda ya ce lalacewar hanyoyi na daga cikin manyan matsalolin da direbobi ke fuskanta.

Ya ce idan aka duba hanyoyin da ke fita daga Kano, misali hanyar Kano zuwa Gwarzo wacce a baya ake yin ta cikin awa biyu zuwa uku, yanzu sai an shafe awa huɗu zuwa biyar saboda lalacewar hanya.

“Gwamnati tana bakin ƙoƙarinta, amma aikin hanyoyin yana tafiya a hankali. Duk hanyar da za ka bi ta fita daga Kano in banda ta Kano-Kaduna zuwa Abuja da ta Wudil zuwa Maiduguri sune da damadama, amma sauran, sai direba ya yi taka-tsan-tsan. Tafiyar da ake yi a awa biyar, yanzu sai an shafe awa bakwai zuwa goma,” in ji shi.

Shugaban ya ce tafiya a hankali na jawo musu karin shan mai da kuma lalacewar motoci, wanda hakan ke jefa su cikin hasara mai yawa. Don haka ya roki Gwamnati da ta gaggauta kammala ayyukan hanyoyin da ake yi domin ci gaban kasa.

Haka kuma, Yakub Haruna ya yaba da kokarin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur na wani lokaci, yana mai cewa matakin ya taimaka. Amma ya ce da a rage farashin da kusan kaso 40 cikin 100 da an fi samun sauki ga direbobi da al’umma baki daya.

Kan batun daukar kaya da ya wuce kima, ya ce kowace mota na da adadin nauyin da ya kamata ta dauka, amma saboda tsadar rayuwa wasu na daukar kaya fiye da kima. Ya ce idan aka yi hanya mai inganci, motoci ba za su lalata hanyar ba, sai dai idan an yi aiki marar inganci.

A karshe, Shugaban na RTEAN reshen Singa ya yi kira ga hukumomi da su tsawatawa jami’an tsaro kan yawan cin zarafin direbobi da yaran mota da suke yi.

Ya ce an samu saukin shingayen da aka dinga kafawa a jihohin Kudu ba bisa ka’ida ba, amma har yanzu ana samun wasu bata-gari da ke karbar makudan kudade a wajen direbobi. Duk dan kasa na da ‘yancin yawo a fadin kasar nan, amma ba daidai ba ne jami’an tsaro su rika cin zarafin direba a kan N200 ko N500. Wannan ba doka ba ce,” in ji shi.

Kwamared Yakub Haruna ya shawarci direbobi da su rika kiyaye dokokin hanya, sannan ya bukaci hukumomi su tabbatar da adalci domin kaucewa cin zarafi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo