Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Sarkin masu maganin gargajiya na al’ummar Marghi a jihar Kano, Alhaji Hassan Usman, ya nuna farin cikinsa bisa nasarar gudanar da gagarumin taron al’ummar Marghi a jihar, wanda ya bayyana a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin kai, soyayya da ’yan’uwantaka a tsakanin al’ummar.
Alhaji Hassan Usman ya bayyana Sarkin Marghi na Kano, Ptil Wadzani Adamu, a matsayin mutum mai tunani da hangen nesa, wanda al’ummar Marghi ke da cikakken aminci da yarda da shi saboda yadda yake tafiyar da jama’a ba tare da nuna bambancin addini ba.
Ya ce Wadzani Adamu mutum ne da yake ɗaukar kowa a matsayin ɗan’uwa, ba tare da la’akari da bambancin addini ko wani abu na daban ba.
Sarkin ya ƙara da cewa ya daɗe bai ga irin wannan gagarumin taro na al’ummar Marghi ba, don haka ya gode wa Allah bisa wannan nasara. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ƙara ɗaukaka al’ummar Marghi a duk inda suke.
Haka kuma, ya roƙi Allah Ya mayar da dukkan ’yan Marghi da abokan arzikin da suka halarci taron domin taya su murna da farin ciki zuwa gidajensu lafiya.
A nasa jawabin, Sarkin Marghi na Zariya, Misari Abdulkarim, wanda ya halarci taron, ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin kai da zumunci a tsakanin al’ummar Marghi.
Ya ce al’adu na da matuƙar muhimmanci wajen haɗa kan al’umma, musamman Marghi da sauran ƙabilun da suke6 zaune tare da su, domin suna taimakawa wajen samar da fahimtar juna da ƙarfafa dangantakar jama’a.
Misari Abdulkarim ya bayyana cewa taron ya nuna cewa al’ummar Marghi ba a bar su a baya ba. Ya ce Ptil Wadzani Adamu ya nuna musu muhimmancin tashi tsaye, rungumar juna da haɗa kai domin raya al’adunsu da tabbatar da cewa ba su ɓace ko su shiga mantuwa ba.
Ya jaddada cewa ya kamata a farfaɗo da al’adun Marghi tare da bunƙasa su, ta yadda ’ya’ya masu tasowa za su san su, su kuma riƙa kwaikwayon kyawawan al’adun kakanninsu.
Sarkin Marghi na Zariya ya ce a yankin Zariya ma suna ƙoƙarin haɗa kan al’ummar Marghi domin raya al’adunsu. Ya bayyana cewa matsalar tsaro da ayyukan ’yan ta’adda ta sa wasu daga cikin al’ummar suka bar garuruwansu suka koma birane, lamarin da ya sa suke ƙoƙarin ci gaba da raya al’adunsu a duk inda suka samu kansu.
A ƙarshe, Misari Abdulkarim ya shawarci matasa da su kasance masu bin kyawawan al’adunsu tare da gudanar da rayuwarsu cikin mutunci da tarbiyya. Ya kuma gargaɗe su da su guji shaye-shaye da shiga ƙungiyoyin da ba su dace ba, domin kare rayuwarsu da makomarsu.






