Al’ummar Margi a Kano Sun Yi Bikin Yawal, Shekara 1 da Nada Ptil Margi

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Al’ummar Margi mazauna jihar Kano sun gudanar da gagarumin bikin al’adunsu na Yawal, tare da murnar cika shekara ɗaya da naɗa Mai Martaba Wadzani Adamu Mamza a matsayin Ptil Margi na Kano.

An gudanar da bikin a ranar Asabar nan da ta gabata, inda aka haɗa bukukuwan gargajiya da na cika shekara ɗaya da hawa karagar sarautar Ptil Margi, tare da naɗa sabbin Bulama da Lawan da za su wakilci sarkin a unguwanni daban-daban.

Taron ya samu halartar sarakuna, jami’an gwamnati, ’yan siyasa, shugabannin ƙabilu daban-daban da kuma ɗumbin al’ummar Margi maza da mata.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, wanda ya halarci taron tare da tawagarsa, ya bayar da gudummawar naira miliyan ɗaya (₦1,000,000) domin tallafa wa gudanar da bikin.

Hon. Doguwa ya bayyana cewa jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana da al’ummomi daban-daban waɗanda suke zaune tare cikin zaman lafiya. Ya ce yana farin ciki da yadda al’ummar Margi suke zaman lafiya da sauran al’ummomin jihar.

Ya bayyana al’ummar Margi a matsayin masu kishin ci gaban al’umma, tare da jaddada muhimmancin kiyaye al’adun gargajiya.

“Raya al’ada yana da matuƙar amfani. Duk inda mutum yake, sanin al’adarsa zai taimaka wajen kiyaye mutuncinsa,” in ji shi.

A nasa jawabin, Mai Martaba Ptil Margi na Kano, Wadzani Adamu Mamza, ya gode wa Allah da kuma daukacin al’ummar Margi bisa amincewa da suka yi da shi, har suka ɗora masa nauyin jagorancinsu.

Ya bayyana ranar a matsayin ta farin ciki, domin kuwa bikin ya haɗa da murnar cika shekara ɗaya da hawansa karagar sarauta da kuma ƙarfafa majalisar gargajiya ta Margi a Kano.

Dangane da kiyaye al’adun gargajiya, sarkin ya yi kira ga iyaye da su ci gaba da magana da ’ya’yansu da harshen Margi domin kada ya ɓace. Haka kuma, ya buƙaci matasa da su riƙa alfahari da sanya kayan gargajiyarsu da kuma gudanar da raye-rayen Margi.

“Idan muka rasa al’adunmu, mun rasa kanmu,” in ji shi.

Da yake magana kan shekara ɗaya da ya yi a kan karagar sarauta, Ptil Margi ya ce ya yi alƙawarin tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba, yana mai cewa an samu nasarori ta hanyar haɗin gwiwar shugabannin al’umma, mata da matasa.

Yayin da yake sanar da naɗin sabbin Bulama da Lawan, sarkin ya jaddada cewa mukaman da aka ba su ba na alfahari ba ne, illa dai nauyin hidimtawa al’umma.

Ya buƙaci waɗanda aka naɗa da su gudanar da ayyukansu cikin tsoron Allah, adalci, tawali’u da gaskiya, tare da kasancewa masu sauƙin kai ga kowa.

“Fadarku ta zama fadar zaman lafiya ga kowa. Kada ku yi amfani da mukaminku wajen zalunci ko karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba,” in ji shi.

Tun da farko, a jawabinsa na maraba, sakataren Ptil Margi na Kano, Mista Zakariya Yusuf Midala Uvu, ya bayyana bikin a matsayin wani muhimmin tarihi ga al’ummar Margi mazauna jihar Kano.

Ya ce bikin Yawal wata hanya ce ta gode wa Allah bisa albarkar girbi, da kuma yin addu’o’in samun zaman lafiya. Ya ƙara da cewa bikin yana koyar da matasa jarumtaka, aiki tuƙuru, gaskiya da mutunta juna.

“Ta hanyar gudanar da wannan biki a nan Kano, nesa da tsaunukanmu, muna bayyana cewa al’adunmu ba za su taɓa mutuwa ba, kuma harshenmu ba zai taɓa ɓacewa ba,” in ji shi.

Mista Uvu ya bayyana cewa a cikin shekara ɗaya kacal, Mai Martaba Wadzani Adamu Mamza ya haɗa ƙungiyoyin Margi ƙarƙashin jagoranci guda, ya samar da kyakkyawar alaƙar zaman lafiya da majalisar masarautar Kano da gwamnatin jihar Kano, tare da farfaɗo da ƙungiyar raya al’adu da kuma ajin koyon harshen Margi ga yaran da aka haifa a Kano.

Da yake bayar da taƙaitaccen tarihin al’ummar Margi a Kano, shugaban ƙungiyar raya al’ummar Margi ta jihar Kano, Elder Apagu Awanuwai Wabba, ya bayyana cewa zuwan Margawa Kano ya samo asali ne tun a shekarun 1940, lokacin da suka fara zuwa domin kasuwanci.

Ya ce dattawan Margi sun kafa ƙungiyar al’ummar a shekarar 1962 a Unguwar Brigade da ke Kano, wadda daga baya ta rarrabu zuwa rassan daban-daban sakamakon ƙaruwar yawan jama’a.

A halin yanzu, al’ummar Margi suna zaune a yankuna daban-daban na Kano, ciki har da Panshekara, Sharada, Bompai, Farawa, Tudun Murtala, Badawa, Rimin Kebe da Darmanawa, inda suke zaune lafiya tare da sauran al’ummomi, suna kuma bayar da gudummawa ga tattalin arzikin jihar.

Elder Wabba ya kuma yi tsokaci kan tarihin warware matsalar sarautar Margi, inda ya ce an fara ɗaukar matakai a shekarar 2018 ƙarƙashin jagorancinsa, lamarin da ya kai ga kafa kwamitin tsakiya.

Bayan rasuwar wanda aka fara zaɓa, marigayi ASP Linus Bello, da kuma jagorancin riƙon ƙwarya da Elder Baba Agwana, tsohon ASP mai ritaya, ya yi a matsayin wakilin Margi a shekarar 2022, kwamitin ya sake zaɓar Wadzani Adamu Mamza a farkon shekarar 2025.

An naɗa Wadzani Adamu Mamza a matsayin Ptil Margi na Kano a ranar 18 ga Oktoba, 2025.

“A cikin shekara ɗaya kacal, Mai Martaba Wadzani Adamu ya tabbatar da cewa ɗan albarka ne. Ya haɗa kan al’ummar Margi, tare da farfaɗo da al’ada, zaman lafiya da manufa guda,” in ji Elder Wabba.

An kammala bikin da raye-rayen gargajiya, baje kolin kayayyakin al’adun Margi da kuma addu’o’in samun tsawon rai ga Mai Martaba Ptil Margi, zaman lafiya a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength