Baburawa 3,500 a Ungogo Na Shirin Ficewa Daga Tafiyar Hon. Sani Adamu

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Magoya bayan Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ungogo da Minjibir, Hon. Sani Adamu Wakili, a Karamar Hukumar Ungogo da aka fi sani da Baburawa, na shirin janye goyon bayan da suke bashi bisa zargin rashin kulawa da su.

Jagoransu a tafiyar NDC Kwankwasiyya, Ibrahim Usman Mshelia, ya bayyana hakan, inda ya ce tun a takarar farko ta Hon. Wakili suke tare da shi, inda suka bada gudunmawa da kudadensu da karfinsu har Allah ya ba shi nasara.

Ya ce kafin zaben 2023, an yi musu zawarci iri-iri da tayin damarmaki don su mara wa jam’iyyar APC baya, amma saboda kaunar da suke wa Wakili suka ki amincewa, suka mara masa baya har ya yi nasara.

“Sai dai abin takaici tsawon shekaru uku babu wani tagomashi da mu Baburawa muka amfana. Duk lokacin da muka koka sai ya ba mu hakuri mu kara saurara,” in ji Mshelia.

Ya kara da cewa abin da ya fi damunsa shi ne yadda ake yi masa gaba da magana cewa duk irin tallafin mashina, motoci da jari da Hon. Wakili ke rabawa, ana ba wa wadanda ko kafar takararsa ba su yi ba, su kuma da suka yi aikin yakin neman zabe ba su samu komai ba.

Mshelia ya ce shi da kan sa ya buga Banoni, Fastoci, rigar fatar kwari da hula da kuma tallafawa mata da matasa domin a zabi Wakili, kuma an zabe shi.

A cewarsa, magoya bayansa na Baburawa sun kai sama da mutum 3,500 kuma yanzu sun zo masa da shawarar cewa tunda ana nemansu a wasu bangarorin siyasa da kyakkyawan alkawari, bai kamata su ci gaba da zama a inda ba a ba su muhimmanci ba.

Ya ce akwai masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC irinsu tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ungogo da wasu manyan mutane a jam’iyyar ADC da ke nemansu, don haka sun ga lokaci ya yi da su je inda ake kaunarsu.

“Allah ya sani mun nuna wa Sani Wakili kauna da goyon baya har ya yi nasara, amma ba a nuna an san da mu ba. Babu amfani mu ci gaba da zama inda ba a ganin kimarmu da darajarmu,” in ji shi.

Ya ce da ace ya daka ta da tuni mutanen nasa sun bar tafiyar, amma shi ne ke ba su hakuri da cewa za a gyara. Amma yanzu sun ga babu sauran mafita illa su tsallaka zuwa inda ake nemansu, tunda siyasa ce.

Ya ce Hon. Wakili da makusantansa irinsu Babawo, Umar, Rabiu Wakili da Nasiru Wakili sun san irin gudunmawar da ya bada, amma yanzu ko wayarsa ba ya dauka.

A karshe ya bayyana cewa sun kammala tattaunawa da mutanensu sama da mutum 3,500 kuma suna shirin yanke hukuncin ficewa daga gidan siyasar Hon. Sani Adamu Wakili a cikin wannan makon.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength