Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Wata ƙungiyar matasan jam’iyyar APC mai suna Coalition of APC Progressive Youth Group ta miƙa ƙorafi ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godwill Akpabio, da Ministan Tsaro, tare da ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International, kan zarge-zargen da ta yi wa Hon. Baffa Babba Ɗan Agundi na aikata abubuwan da ta ce sun saɓa wa doka.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta miƙa ƙorafe-ƙorafen ne a ranakun 30 ga Oktoba da 2 ga Nuwamba, 2026, inda aka tabbatar da karɓar takardun a ranar 5 ga Nuwamba.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Salisu, ya sanya wa hannu tare da rabawa manema labarai a Kano.
A cewar Salisu, matakin na da nufin jawo hankalin hukumomin gwamnati da Majalisar Tarayya kan abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin yunƙurin nuna fin ƙarfin doka da kuma rashin bin ƙa’idojin hukumomi da take zargin Ɗan Agundi da aikatawa.
Ya bayyana cewa kai ƙorafin ga Amnesty International wani ɓangare ne na ƙoƙarin bin diddigin koken da ƙungiyar ta ce ta riga ta miƙa wa Shugaban Majalisar Dattawa da Ministan Tsaro, domin ganin an gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace.
Ƙungiyar ta kuma zargi Ɗan Agundi da shirya wata zanga-zanga ba bisa ƙa’ida ba, da nufin sake tayar da rikicin sarautar Kano, ta hanyar nuna goyon baya ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, duk da cewa batun na gaban kotu. Salisu ya ce irin wannan mataki na iya zama ƙalubale ga hukumomin da ke da alhakin tabbatar da doka da oda.
A cikin sanarwar, Salisu ya zargi ɗan siyasar da hannu wajen ayyukan da ya ce sun nuna rashin biyayya ga hukumomi, yana mai cewa: “Halayen nuna fin ƙarfin doka da ɗaukar doka a hannu ne suka janyo aka je aka fasa allunan Shugaban Ƙasa da na Gwamna.”
Ya ƙara da zargin cewa ana amfani da rikicin masarautar wajen ƙarfafa ayyukan daba da tashin hankali a siyasa, yana mai gargaɗin cewa tara matasa bisa bambancin ra’ayin siyasa na iya zama barazana ga tsaron jama’a da zaman lafiyar ƙasa.
A ƙarshe, Sakataren ƙungiyar ya ce ba za su ci gaba da yin shiru kan abin da ya kira raina doka ba, inda ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike na gaskiya da adalci, tare da ɗaukar matakin da ya dace idan binciken ya tabbatar da zarge-zargen. Ya ce hakan zai taimaka wajen kare martabar doka da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano.
Duk ƙoƙarin da Wakilinmu ya yi don jin ta bakin wanda ake zargi, Babba Ɗan Agundi, abin ya tura, sai dai duk lokacin da muka same shi za ki ji ta bakinsa.






