Taron Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Tarauni Dama Ce Ta Zumunci Da Bunƙasa Cigaba -Abba Danguguwa

Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Babban Sakatare na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Abba A. Danguguwa, ya bayyana taron haduwar tsofaffin daliban makarantar firamare ta Tarauni Special, ajin 1986, a matsayin wani taro mai albarka kuma mai cike da mu’amala mai ma’ana ta zumunci da bunkasa cigaba.

Alhaji Danguguwa, wanda shi ma tsohon dalibi ne na makarantar, ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a yayin taron haɗuwar da kuma gabatar da tallafin ci gaban makaranta da aka gudanar ranar Asabar a harabar makarantar.

A cewarsa, wannan taro ya tattaro mutane daga nesa da kusa waɗanda a wani lokaci suka taɓa zama tare a aji ɗaya, kuma yanzu suka sake haɗuwa bayan shafe shekaru masu yawa, kowannensu ya zo da irin ƙwarewa da ilimi da ya samu a fannonin sana’o’insu daban-daban domin yin mu’amala da musayar ra’ayoyi.

“A haƙiƙanin gaskiya, wannan dandali ne da ya ba da damar auna ci gaba da nasarorin da aka samu a cikin shekaru 40 da suka gabata. Wani lokaci ne na addu’a da tunani,” in ji shi.

Ya bayyana cewa wannan taro kira ne ga ƙananan yara masu zuwa makaranta da su ga manyansu waɗanda suka ci gaba a rayuwa domin su yi koyi da su su zama cikin nagartattun mutane a cikin al’umma.

Da yake magana kan ilimi, Babban Sakataren ya ce babu shakka idan ana maganar ilimi ana magana ne kan yadda ilimi zai kyautata mai inganci ga wata A ilimi shi ne ginshikin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, amma saboda matsaloli da tabarbarewar tattalin arziki, ilimin yana tabarbarewa ingancinsa ba kamar a baya ba

“Amma Gwamnatoci a karkashin shugabannin da akayi a baya da na yanzu tana yin abin da ya kamata domin tabbatar da ingancin ilimi ga yaranmu, kuma abin a yaba ne kwarai,” in ji Alhaji Abba A. Danguguwa.

Babban sakataren na ofishin shugaban ma’aikatan Gwamnatin jihar Kano.Alhaji Abba A Danguguwa na daga cikin tsofaffin daliban ajin 86 da aka karrama da takardar yabo bisa gudummawar da ya bayar ga makarantar.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo