Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Kwamishinan Gidaje da Bunƙasa Birane na Jihar Kano (Housing Development), Arch. Ibrahim Yakub Adamu Garko, ya bayyana taron da masu harkar gidaje da filaye na Kano Real Estate suka shirya a matsayin wani muhimmin taro da ya dace da mahimmancin Kano a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Arch. Garko ya ce taron ya haɗa ‘yan kasuwa da ɓangaren gwamnati domin tattaunawa kan harkar Real Estate, wato gine-gine da gidaje da makamantansu.
Ya ce Allah ya albarkaci Kano da cigaba sosai a fannin gine-gine, har darajar ƙasa a Kano ta kai har ma ta wuce ta Abuja a wasu wurare. Don haka ya kamata a riƙa irin wannan tattaunawa domin jama’a su san abin da gwamnati ke yi, sannan masu zuba jari su bayyana abin da suke buƙata daga gwamnati domin haɗa hannu wajen rage matsalar ƙarancin gidaje a ƙasa.
“Manufar ita ce a gina gidaje masu yawa da kowa zai iya saya cikin sauƙi, sannan a tsaftace harkar domin daƙile hanyoyin da ba su dace ba a harkar gidaje,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce ya ji daɗin ganin yadda ‘yan jihar Kano suka fara shiga harkar samar da gidaje, yana mai fatan za a ci gaba da gudanar da irin wannan taro duk shekara domin warware matsalolin harkar gidaje na manya da ƙanana.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ɓullo da sabbin tsare-tsare a fannin gidaje, ciki har da raba Hukumar Tsara Birane da Filaye (KNUPDA) zuwa hukumomi biyu.
Hukuma ɗaya za ta riƙa bayar da izinin gini cikin sauƙi da sauri, yayin da ɗayar kuma za ta riƙa bibiya da kulawa wajen tabbatar da an bi ka’idojin izinin da aka bayar.






