Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazaɓar Gwale a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Hon. Abdulhadi Dalhatu Awilo, ya bayyana cewa shi ne halastaccen ɗan takarar jam’iyyar a mazaɓar, wanda shugabancin jam’iyyar ya tabbatar, sannan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da sunansa.
Awilo ya bayyana cewa NDC ce jam’iyyar da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zaɓa domin ciyar da tafiyar siyasar sa gaba, yana mai cewa jam’iyyar ce za ta samar da sauƙi ga talakawa tare da ba su damar cin moriyar dimokuraɗiyya.
Ya bayyana cewa a baya ya yi takarar majalisar dokokin jihar a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023. Sunnan ya zama shugaban PDP na Gwale a shekarar 2024. Daga bisani, sun shiga jam’iyyar ADC bayan haɗin kan magoya baya daga ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, amma sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka samu a jam’iyyar, sai Kwankwaso ya zaɓi NDC, lamarin da ya sa suka koma jam’iyyar baki ɗaya, wanda a cewarsa ya ƙara mata ƙarfi.
Da yake tsokaci kan siyasar Kano, Awilo ya ce rabuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoransa Kwankwaso babban ƙalubale ne ga gwamnan, musamman ganin cewa ya koma APC, jam’iyyar da ya ce al’umma ba su gamsu da mulkinta ba sakamakon matsin tattalin arziƙi da suka fuskanta tun zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari har zuwa yanzu.
Ya ce, “An samar da NDC ne domin talaka ya ɗanɗani romon dimokuraɗiyya. Mun fitar da Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, tare da Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa za su kawo ci gaba mai ɗorewa a ƙasar nan.”
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta tsayar da Kwamared Aminu Abdussalam a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano, yayin da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso yake takarar mataimakin gwamna, yana mai cewa haɗin kansu zai ba magoya bayan Kwankwasiyya damar ci gaba da tafiyarsu ta siyasa.
Ɗan takarar ya bayyana cewa idan aka zaɓi Aminu Abdussalam da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matakin gwamna da mataimakinsa, tare da zaɓensa a matsayin ɗan majalisar Gwale da sauran ’yan takarar NDC a ƙananan hukumomi 44, za su samar da ayyukan raya ƙasa da za su amfani al’ummar Kano baki ɗaya.
Ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar NDC da ba su samu tikitin takara ba da su haƙura, su haɗa kai domin samun nasarar jam’iyyar, yana mai cewa manufar siyasa ita ce yi wa al’umma hidima da kawo ci gaba, ba biyan buƙatun kai kawai ba.
Awilo ya ce duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ɗan asalin Gwale ne, ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a ƙaramar hukumar ba su taka kara suka karya ba balle su gamsar da al’umma ba, musamman ta fuskar magance rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa, waɗanda a cewarsa ke taimakawa wajen yawaitar faɗan daba.
Ya ce al’ummar Gwale na buƙatar sabon tsarin shugabanci da zai magance waɗannan matsaloli.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Gwale da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan takararsa, yana mai jaddada cewa jam’iyya ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takararta sau uku, sannan INEC ta fitar da sunansa.
Ya roƙi al’umma da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu ranar zaɓe domin zaɓar ’yan takarar NDC daga sama har ƙasa, yana mai cewa yana da yaƙinin jam’iyyar za ta samu nasara a zaɓe mai zuwa, da yardar Allah.





