JNC Ta Horas Da Ma’aikata 500 Kan Sana’o’in Dogaro Da Kai A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Majalisar Sasanta Matsalolin Ma’aikata ta Ƙasa (JNC), reshen jihar Kano, tare da haɗin gwiwar Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano, ta shirya taron horaswa na kwana biyu ga ma’aikata kusan 500 da ke dab da yin ritaya, domin koya musu sana’o’in dogaro da kai bayan barin aiki.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban JNC reshen Kano, Kwamared Hashim A. Saleh, ya ce tun a shekarar 2024 ne suka nemi haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kano ta hannun Ofishin Shugaban Ma’aikata, inda suka haɗu da masana da suka riga suka yi ritaya da kuma waɗanda har yanzu ke aiki, suka samu ilimi, sannan suka ga dacewar dawo da wannan ƙwarewa jihar Kano domin taimaka wa ma’aikatan da ke shirin barin aiki a bana.

Ya bayyana cewa, duk da wasu na ganin an makara wajen fara irin wannan shiri, hakan ba gaskiya ba ne, domin a cikin watanni uku zuwa huɗu ana iya koyar da ilimin sana’a da zai sa ma’aikaci ya fara tunanin yadda zai dogara da kansa kafin ya kammala aikinsa.

Kwamared Saleh ya ƙara da cewa, ba tare da neman tallafin kuɗi daga gwamnatin jihar ba, JNC ta tattara kuɗaɗe daga cikin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta, tare da shirya taron na kwana biyu domin faɗaɗa wannan tsari a jihar Kano.

Ya ce mahalarta taron guda 500 za su samu horo da shaidar kammalawa a fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, harkar lafiya, sadarwar zamani da kuma sana’o’in kasuwanci.

Bayan kammala horaswar, za a kai su ƙananan masana’antu domin ganin yadda ake gudanar da ayyuka a aikace.

A cewarsa, “Ba ma son ganin ma’aikaci ya bar aiki ya wayi gari bai san inda zai dosa ba. Wannan ne babban dalilin shirya wannan taro.”

Ya kuma bayyana aniyar faɗaɗa shirin nan gaba, tare da kira ga gwamnati ta ƙara ba da gudummawa.

Ya yaba da irin kulawar da gwamnatin jihar Kano ke bai wa ma’aikata, ciki har da ɗaukar sabbin ma’aikata, biyan albashi cikin lokaci, da aiwatar da ƙarin girma.
Sai dai ya buƙaci gwamnati ta sake duba batun bashin da ake bai wa ma’aikata na Naira 300,000, yana mai cewa adadin bai dace da halin tsadar rayuwa ba, musamman wajen sayen mota ko babur.

Haka kuma ya roƙi a duba batun ƙarin albashi bisa tanadin dokar ƙasa.

Kwamared Hashim A. Saleh ya kuma roƙi Gwamnan jihar Kano da ya tallafa wa JNC da fili da za su gina cibiyar horaswa ta dindindin ga ƙungiyoyin ma’aikata, maimakon ci gaba da neman wuraren wucin gadi.

Ya ƙara da roƙon a ba ƙungiyar mota domin sauƙaƙa zirga-zirgar ayyukansu.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC), kuma shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Ƙasa, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, wanda ya bayyana jin daɗinsa da shirya bitar.

Ya ce shirin abin a yaba ne, kuma ya kamata a faɗaɗa shi zuwa matakin ƙasa, domin kowane ma’aikaci ya san cewa wata rana zai bar aiki, ko ta hanyar kai shekarun ritaya ko wasu dalilai.

Ya yi kira ga ƙungiyoyin ma’aikata da su ci gaba da fito da irin wannan tsari, tare da alƙawarin ɗaukar batun zuwa shugabancin ƙasa na ƙungiyarsa domin faɗaɗa shirin zuwa dukkan jihohin Najeriya.

A nasa jawabin, Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Musa, ya ce gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da biyan haƙƙin ’yan fansho yadda ya kamata, tare da kawo tsare-tsare da za su tabbatar da cewa ma’aikacin da ya kammala aikinsa cikin lokaci zai samu kuɗaɗen sallamarsa ba tare da jinkiri ba.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da bullo da tsare-tsaren da za su ƙara kyautata walwalar ma’aikata a jihar.

  • Related Posts

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Asibitin Ƙashi na Tarayya da ke Dala, Kano, ya ba wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi, Hon. Abba Kabir Bichi, lambar karramawa bisa gudunmawa…

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gidauniyar NNPCL, reshen ayyukan jin ƙai na NNPC Ltd, ta ƙaddamar da sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani mai ƙarfin 1.5 Tesla MRI Scan da aka…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity