Daga Ibrahim Muhammad Kano
Cibiyar sayar da magunguna ta Kanawa da ke Kasuwar Ɗangwauro a jihar Kano ta musanta wani labari da ake yaɗawa cewa an kama haramtattun magunguna a cikin kasuwar.
Shugaban ƙungiyar Pharmaceutical Partners ta kasuwar Ɗangwauro, Alhaji Husaini Labaran Zakari, ne ya bayyana hakan yayin da yake ƙaryata zargin.
Alhaji Husaini Labaran Zakari ya bayyana cewa gaskiyar abin da ya faru shi ne an shigo da wani magani da aka ƙera domin jinyar masu larurar kwakwalwa, irin wanda ake amfani da shi a manyan asibitoci.
Sai dai ya ce wasu matasa masu shaye-shaye sun fahimci tasirin maganin, inda suke sayensa suna amfani da shi ba tare da izinin likita ba domin ya jawo musu maye.
Ya ƙara da cewa cibiyar tana da cikakken bayani kan adadin maganin da ake buƙata a asibitocin jihar Kano.
Saboda haka, sai suka yi mamakin ganin an shigo da adadi mai yawa fiye da yadda ake buƙata.
Duk da haka, ya tabbatar da cewa wanda ya shigo da maganin ya bi dukkan ƙa’idoji da sharuɗɗan doka na hukumomin da suka dace.
A cewarsa, a yawancin lokuta, ba a fi buƙatar kati biyar zuwa goma na irin wannan magani a duk faɗin jihar Kano ba. Amma sai aka shigo da kimanin kati 200, wanda hakan ya jawo damuwa, musamman ganin cewa akwai yiwuwar maganin ya faɗa hannun matasa masu amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.
Alhaji Husaini ya ce wannan ne ya sa suka sanar da jami’an tsaro da kuma jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), inda aka karɓe magungunan aka miƙa su ga hukumomin da suka dace domin kauce wa yiwuwar amfani da su ba bisa ƙa’ida ba, wanda zai iya haifar da illa ga al’umma.
Ya jaddada cewa maganin ba haramtacce ba ne, kuma ba a ƙera shi domin cutarwa ba.
Sai dai kamar yadda yake da dukkan magunguna, idan aka yi amfani da su ba tare da umarnin likita ba, za su iya haifar da illa.
Ya yi bayanin cewa ko masu larurar ƙwaƙwalwa ana ba su ƙwaya ɗaya ne bisa ƙa’ida, amma idan lafiyayyen mutum ya sha fiye da haka, hakan na iya haifar da matsaloli masu tsanani.
Ya kuma bayar da misali da wani maganin tari da ake kira Codeine, wanda a baya ake amfani da shi domin jinya, amma daga baya wasu matasa suka riƙa amfani da shi wajen shaye-shaye, lamarin da ya sa gwamnati ta haramta shi gaba ɗaya domin kare lafiyar jama’a.
Alhaji Husaini Labaran Zakari ya ce tun bayan dawowar masu sayar da magunguna zuwa kasuwar Ɗangwauro, sun fahimci manufar gyaran da gwamnati ta kawo, kuma yanzu suna ba da cikakken goyon baya domin tabbatar da an gudanar da harkokin sayar da magunguna bisa ƙa’ida.
Ya ƙara da cewa sakamakon wayar da kan jama’a da ake yi, mutane sun fara fahimtar muhimmancin amfani da magunguna yadda ya kamata.
Ya ce duk wanda yake cikin harkar magunguna yana da alhakin kare lafiyar kansa da ta sauran jama’a, domin rashin kulawa na iya jawo illa ga al’umma.
A ƙarshe, Alhaji Husaini Labaran Zakari ya gode wa gwamnati da hukumomin da abin ya shafa bisa goyon bayan da suka bayar wajen gyara harkar saye da sayar da magunguna.
Ya ce wannan nasara ta kowa ce, wato gwamnati, masu sayar da magunguna da kuma al’umma baki ɗaya, domin manufarta ita ce kare lafiyar jama’a da tabbatar da cewa ana amfani da magunguna cikin aminci da bin doka.







