Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Anka

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada ƙudirin sa na tabbatar da cewa jihar Zamfara ta shiga sahun jihohin da ke kan turbar ci gaba mai ɗorewa da amfanar al’umma baki ɗaya.

A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da manyan ayyukan raya ƙasa guda huɗu a Ƙaramar Hukumar Anka, a wani mataki da ke nuna cikar alƙawuran da ya ɗauka ga al’ummar yankin.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da sake gina da kuma cikakken gyaran fadar Sarkin Zamfaran Anka tare da saka kayan zamani, fara aikin titin Anka–Abbare, da kuma gina sabuwar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Anka.

Sauran ayyukan da aka fara sun haɗa da gina ofisoshin Hukumar Hisbah da Rundunar Kare Al’umma (CPG), tare da sake gina makarantar SAFE School da ke Anka domin samar da yanayi mai tsaro da inganci ga ɗalibai.

A jawabin da ya gabatar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ziyarar tasa zuwa Anka na daga cikin cika alƙawuran yaƙin neman zabensa ga al’ummar Anka da ma jihar Zamfara baki ɗaya.

Ya ce ƙaddamar da sabuwar fadar Sarkin Anka da Majalisar Sarakunan Zamfara na daga cikin muhimman matakan da ke mayar da martaba da kimar masarautun gargajiya, waɗanda su ne ginshiƙan al’ada da tarihi.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa fara aikin titin Anka–Abbare zai inganta hanyoyin zirga-zirga zuwa yankunan karkara, ya bunƙasa kasuwanci, tare da samar da tasirin tattalin arziki mai yawa ga al’umma.

Ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin ceto Zamfara shi ne dawo da kima, daraja da nagartar aikin gwamnati ta hanyar samar da ingantaccen wurin aiki ga ma’aikata a matakin jiha da na ƙananan hukumomi. Saboda haka ne aka fara gina sabon sakatariyar ƙaramar hukuma a Anka.

Gwamnan ya bayyana cewa babu wata al’umma da za ta ɗore ba tare da bin doka da oda ba, don haka samar da ofisoshi ga Hisbah da CPG zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Dangane da ilimi, Gwamna Lawal ya ce ilimi shi ne ginshiƙin kowace al’umma mai tasowa, don haka sake gina SAFE School a Anka wani bangare ne na shirin gaggawa na samar da muhalli mai tsaro da dacewa ga ɗalibai.

Ya ƙara da cewa, bayan maddamar da ayyuka a masarautar Anka da Tsafe, nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da ayyuka a Kaura Namoda da Moriki. Haka kuma ayyuka a Bungudu, Bukkuyum da Zurmi na gudana kuma za a kammala su tare da ƙaddamar da su kafin ƙarshen shekarar nan, In Sha Allah.

Related Posts

Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani