Zamanin Cin Zarafin Ma’aikata Ya Ƙare, Gwamnatina Ta Gaskiya Da Riƙon Amana Ce -Gwamna Abba Kabir Yusuf

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana takaicinsa kan rahotannin da suka nuna ana rage albashin wasu ma’aikatan gwamnati, ko kuma hana su albashinsu gaba ɗaya, yana mai cewa hakan babban cin zarafi ne ga haƙƙin ma’aikata, kuma cin amanar jama’a.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

Gwamna Yusuf, wanda ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan labarin cewa wasu ma’aikata sun kwashe watanni ba tare da an biya su haƙƙinsu ba, ya yi alƙawarin binciko masu hannu a wannan aika-aikar, tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansu.

“Wannan gwamnati ba za ta lamunci zalunci ga ma’aikata ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika, doka za ta yi aiki a kansa ba tare da rangwame ba,” in ji Gwamnan.

A wani mataki na kawo ƙarshen wannan matsala, Gwamnan ya ƙaddamar da wani kwamitin bincike mai ƙarfi don gano musabbabin matsalar, ko dai matsalar fasaha ce, ko kuma ganganci da gangan da wasu suka aikata.

Kwamitin zai gudanar da bincike na musamman kan albashin ma’aikatan gwamnati daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025, domin gano waɗanda abin ya shafa, tantance irin asarar da aka yi, tare da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Kwamitin mai mambobi bakwai, wanda Hon. Abdulƙadir Abdussalam, Kwamishinan Harkokin Karkara da Ci gaban Al’umma, kuma tsohon Akanta-Janar na Jihar Kano ke jagoranta, ya ƙunshi ƙwararru a fannin kuɗi da tsarin biyan albashi.

Ga cikakken jerin mambobin kwamitin:l

  1. Hon. Abdulkadir Abdussalam – Shugaban Kwamitin
    Kwamishinan Harkokin Karkara da Ci gaban Al’umma
  2. Dr. Bashir Abdu Muzakkari – Memba
    Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Tattalin Arziƙin Zamani (Digital Economy)
  3. Dr. Aliyu Isa Aliyu – Memba
    Daraktan Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano
  4. Dr. Hamisu Sadi Ali – Memba
    Daraktan Hukumar Sarrafa Basussuka ta Jihar Kano
  5. Hajiya Zainab Abdulƙadir – Memba
    Daraktar Cibiyar Kwamfuta ta Jihar Kano
  6. Aliyu Muhammad Sani – Sakataren Kwamitin
    Daraktan Bincike da Tantancewa, Ofishin Sakataren Gwamnati
  7. Ummulkulthum Ladan Kailani –Mataimakiyar Sakataren Kwamitin
    Babbar Mataimakiyar Sakataren Gudanarwa, Ofishin Sakataren Gwamnati

An ba wa kwamitin wa’adin kwana bakwai kacal domin ya kammala bincikensa tare da gabatar da cikakken rahoto kan masu hannu a lamarin, girman ɓarnar da aka yi, da kuma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki don tabbatar da adalci, gaskiya, da biyan albashi cikin lokaci, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi ba zai tsira ba.

“Zamanin cin zarafin ma’aikata ya ƙare. Wannan gwamnati ce ta gaskiya da riƙon amana, kuma duk wani da aka samu da hannu a wannan aika-aika ba zai tsira ba,” in ji Gwamnan.

Kwamitin binciken na fatan gano duk wata badaƙala da aka tafka a tsarin biyan albashi, tare da dawo da martabar tsarin albashi a Kano domin kare haƙƙin ma’aikata.

Sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruƙ Ibrahim ne ya ƙaddamar da kwamitin a madadin mai girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?