Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP da cewa tamkar ruwan jakara ne da kowa ya sha domin gyaran tsohon nama.

Hon. Shuwaki ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen taron kaddamar da shugabannin riko na jam’iyyar PDP na jihar Kano da aka gudanar a Gidan Mumbayya.

Ya ce tun bayan da PDP ta bar mulki, Najeriya ta shiga cikin mawuyacin hali na tsananin kuncin rayuwa.

Ya ce suna tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa idan suka sake zaben PDP, musamman a jihar Kano, za su dawo da martabar Kano da ta kasuwancinta, tare da samar da ayyukan yi na gari ga matasa.

Da yake bayanin dalilinsa na barin APC, Hon. Shuwaki ya ce: “Na bar jam’iyyar APC ne saboda irin zaluncinta da yadda ta lalata kasar nan, ta jefa al’umma cikin kunci.”

Ya yi kira ga al’ummar kasa baki daya, musamman na jihar Kano, da su guji jam’iyyar APC su koma jam’iyyar PDP domin samun sauki.

” A lokacin da PDP ta bar mulki, Dala tana Naira 120, buhun siminti bai kai Naira 2,000 ba, amma yanzu a duba yadda abubuwa suka yi tsada, sun gagari talaka. Mai karamin karfi sai wahala yake sha,” in ji shi.

Ya karkare da cewa yana da cikakken yakinin cewa al’ummar karamar hukumar Tudun Wada za su marawa jam’iyyar PDP baya dari bisa dari a zabe mai zuwa.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum