PRP Za Ta Yi Aiki Tuƙuru Domin Kawar Da Zalunci A Ƙasar Nan -Abba Sule Namatazu

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa a tsarin ƙasar nan tun 1999, kusan tafiyar jam’iyyar ɗaya ake yi, sai dai idan lokaci ya zo sun fahimci mutane sun gane abin da ake nufi, sai a sauya mata suna ta ƙarfafa wata jam’iyyar, Injiniya Abba Sule Namatazu mataimakin shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa mai kula da shiryar Arewa maso Yamma ne ya bayyana hakan a taron da jam’iyyar ta gudanar a ranar Asabar a ɗakin taro na Mumbayya.

Ya ce, “A baya sunan jam’iyyar da ke mulkin ƙasa ita ce PDP, sai aka yi bula-bula ta koma APC. Mun ce jam’iyya ɗaya ce. Saboda daga 1999 da mulkin farar hula ya dawo, an ɗan kwatanta zaɓuɓɓuka a ƙananan hukumomi. A wancan lokacin jam’iyyu daban-daban sun sami shugabanni na ƙananan hukumomi da kansiloli.

“Daga nan aka kafa ginshiƙi na ruguza tsari na jam’iyyu da yawa. Haka ake ta tafiya har aka kawo yanzu abin da suke so su yi irin abin da aka yi a yi lokacin Abacha, duk jam’iyyu su haɗu su ce sun tsayar da Tinubu shi ne tsarin da aka nufa,” in ji shi.

Namatazu ya ce, “Mutanen ƙasar nan yanzu jikinsu ya gaya musu, sun san babu yadda za a yi a tsayar da jam’iyyar APC da wata jam’iyyar ta kirki a ce ta kai labari, idan kuwa akace mutum ɗaya ne duk jam’iyyu sun haɗu sun fiitar da shi takara, ka ga ruwa ta sha ke nan a wajensu.”

Ya ƙara da cewa, “Masu kira a zo a yi haɗaka domin a kayar da APC, duk cikinsu idan aka duba waye ke da bambanci da APC ɗin? Wani ya yi Gwamna ko Minista ko Ɗan Majalisa ko Shugaban ƙaramar hukuma ko Kansila. Ba Tinubu ne kaɗai ya jefa ƙasar nan a halin da take a ciki ba.”

Ya ce, duk wanda ya yi Gwamna daga 1999 ko ya riƙe wani muƙami, su suka haɗu suka jagula da lalata ƙasar nan. “Waɗanda suka haɗu suka lalata ne kuma za su dawo su ce wane ya fi dama-dama? Duk irin su ɗaya ne,” ya jadadda.

Injiniya Abba Sule Namatazu ya ce jam’iyyarsu ta PRP ba lallai ne ta shiga cikin wannan kwamacala tasu ba, dama faɗa ne ake tsakanin Ɗanjuma da Ɗanjummai.

Ya ce taron da suka gudanar na jam’iyyar a Kano sun duba halin da jam’iyyar tasu take ciki ne da halin da ƙasa ta shiga shekaru 26 bayan dawowar mulkin farar hula.

Ya tabbatar da cewa a matsayin PRP ta daɗaɗɗiya jam’iyya mai aƙida da kishin talaka, za ta yi duk mai yiwuwa wajen haɗa kan ‘ya’yanta da buɗe ƙofa ga mutane masu kishi da aƙida su shigo a farfaɗo da martabarta a Kano da Arewa da ƙasa baki ɗaya.

Ya ce a yanzu shugabannin riƙo ne ke riƙe da jam’iyyar. Nan gaba za su gudanar da babban taro na masu ruwa da tsaki don a samar da zaɓaɓɓun shugabanni na kowane mataki da za su yi aiki tuƙuru domin kawar da zaluncin da ake yi a ƙasar nan.

Taron dai ya sami halartar ɗimbin ‘ya’yan jam’iyyar maza da mata da shugabannin jam’iyyar daga jihohin Kano, Jigawa da Kaduna da wasu da suka taɓa yi mata takara a matakai daban-daban a zaɓen da ya gabata.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum