Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnatin jihar Kano, ta amince da fitar da sama N87,000,000 domin aiwatar da aikin sanya ‘interlock’ a Sakatariyar mulki ta ƙaramar hukumar Dala.
Wannan na ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannu
Hassana Aminu,
Jami’ar yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Dala.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da aikin. Ya ce an kafa sakatariyar ƙaramar hukumar Dala ne tun a shekarar 1989, kuma tun daga lokacin ba ta samu wani sauyi ba har sai yanzu.
Ya bayyana cewa aikin yana daga cikin manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na kawo sauyi da cigaba.
“Kuma kamfanin da zai gudanar da aikin, tuni an biya wani kaso daga cikin kuɗin aikin, da ake sa ran kammala aikin cikin wata guda,” in ji shi.
Baya ga shimfida interlocin, Shugaban ƙaramar hukumar Dala Hon. Suraj Imam ya ce, akwai shirin yi wa sakatariya fenti da sauya mata ƙofofi, da gina sabuwar katanga, da gina sabuwar majalisar kansiloli.
Ya ce akwai kuma yiwuwar sanya fitila mai aiki da hasken rana a dukkanin ofisoshin ma’aikata.
Alhaji Surajo Imam ya gode wa Majalisar Kansiloli bisa yadda suke ba shi goyon bayan a kan duk wani shiri na ci gaban al’umma.
Ya ƙara da cewa wannan aiki yana daga cikin ɗimbin alherin da gwamnatin Kano ke aikatawa ga jama’a bayan sun miƙa buƙatunsu.
A nasa ɓangaren, Shugaban Sashin Ayyuka na ƙaramar hukumar Dala, Alhaji Shafi’u Musa Gwarzo, ya bayyana farin cikinsa da ƙaddamar da wannan muhimmin aiki.
Ya yi kira ga ma’aikata da su kula da kayan aikin da aka samar domin amfani da su yadda ya kamata, tare da tabbatar da ɗorewarsu.






