Gwamnatin Kano Ta Buƙaci Ƙirƙiro Sabuwar Jiha Da Ƙarin Ƙananan Hukumomi

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnatin jihar Kano ta gabatar da muhimman buƙatu ga Kwamitin Majalisar Wakilai na gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa, ciki har da buƙatar ƙirƙirar sabuwar jiha daga cikin Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta bakin mataimakinsa, Injiniya Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gabatar da buƙatun ne a yayin taron jin ra’ayin jama’a na yankin Arewa maso Yamma da ya gudana a Kaduna.

A cewa gwamnatin Kano, lokaci ya yi da za a sake fasalin tsarin mulki don bai wa jihohi damar bunƙasa bisa sahihin tushe. Daga cikin buƙatun da aka gabatar akwai:

Kirkiro sabuwar jiha daga cikin Kano, don rage cunkoso da ƙarfafa wakilci.

Ƙara yawan ƙananan hukumomi a jihar Kano tare da tabbatar da cikakken ‘yancinsu.

Samar da ‘yan sandan jihohi, domin inganta tsaro da ingantaccen amsa ga matsalolin tsaro na cikin gida.

Sake fasalin rabon tattalin arziƙin ƙasa, ta yadda za a samu daidaito tsakanin jihohi wajen amfani da albarkatun ƙasa da kuɗaɗen shiga.

Gwamnan ya jaddada cewa buƙatun sun fito ne daga muradun al’ummar Kano, kuma gwamnati na da ƙwarin gwiwar cewa Majalisar za ta ɗauki matakin da ya dace domin tabbatar da sauye-sauyen da ake nema.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo