Daga Wakilinmu
Majalisar Matasan Afrika Don Zaman Lafiya da aka fi sani da African Youth Assembly for Peace (AYAP), ta karrama manajan daraktan Kamfanin Sadex Engineering Nigeria Limited, Injiniya Iliyasu Usman Salisu da lambar yabo na zama Jakadan zaman lafiya na Africa, a ranar 10 ga Yuli, 2025.
Da take karanta tarihin wanda aka karrama a yayin gudanar da taron mamba mai kula da harkokin mata ta ƙungiyar ta AYAP, Alhaqqat Hussain Babaji ta bayyana cewa, an haifi Injiniya Ilyasu Usman Salihu a ranar 7 ga Fabrairu, 1968 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano. Ya fara karatu a garin na Gaya. Sannan ya ci gaba da karatu a Kwalejin Fasaha ta Gwamnati (GTC) da ke Wudil.
Ya taso ne a unguwar Tudun Wada da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano. Daga nan ya aza ginshikin ayyukansa cigaban rayuwa.
Injiniya Iliyasu Usman mutum ne mai ƙoƙari da ya sami nasarori a fannoni daban-daban na harkokin gina kasuwanci da masana’antu da harkokin kwangila da samar da sana’o’i.
Ya kuma riƙe mayan mukamai a harkar gudanarwa da harkokin masana’antu da kasuwanci ciki har da darakta a manyan kamfanoni da yawa a cikin Nijeriya da suka haɗa da a Philko Ltd. Sadex Engineering Ltd. Gongola Power Holding Company (GCPL), Magnets International Ltd. Granite Builders. Yewtawa Sovereign Resources Nigeria Ltd.
Ta ƙara da bayyana Injiniya Iliyasu Usman Salihu a matsayin Jagora a siyasa da mai son bunƙasa cigaban matasa da tausayi da jin ƙai, ya riƙe muƙamai daban-daban na siyasa a matakin ƙasa da waje.
“Irin ƙoƙarinsa na ƙarfafa matasa ta sa ya sami lambobin yabo da dama daga ƙungiyoyi a matakin ƙasa da waje.
Mutum ne mai taimakon jama’a, wanda ya cancanci yabon da yake samu a tsakanin matasa, mata da ƙananan yara, marayu da masu rangwamen gata saboda kyawawan ayyukansa na alheri
Injiniya Iliyasu Usman Salihu a muƙami na siyasa shi ne tsohon sakataren jam’iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Nasarawa, kuma a halin yanzu sakataren dattawan jam’iyyar na ƙaramar hukumar.
“Mutum ne mai son kawo sauyi da yake duƙufa da jajicewa wajen taimakawa matasa da ƙoƙarin kange su daga hana su yin abin da bai dace ba, domin su zama masu amfani ga al’umma, tare da ɗora su a kan yin sana’o’i. Irin ƙwazo da ƙwarewarsa a matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Matasan Nijeriya (NYO) na ƙasa da kuma irin taka rawa a harkokin haɗa kai da inganta matasa a ƙasa sun ba shi damar ƙoƙarin bunƙasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin Afirka,” in ji ta.
Alhaqqat Hussain Babaji ta ce, “Wanda muke bai wa lambar yabo a yau uban ne, jagora mai kyawawan halaye da ɗabi’u, abin koyi da Ƙungiyar Matasan Afrika masu fafutukar tabbatar zaman lafiya suka zo don haɗa kai da shi a matsayinsa na jagora mai hangen nesa da kyakkyawan tunanin bunƙasa cigaban al’umma musamman matasa.”
Ta ƙarƙare bayanin da taya murna ga wanda aka bai wa lambar yabon Injiniya Iliyasu Usman Salihu bisa nasarar da ya samu ta tabbatar da shi a matsayin Jakadan Zaman Lafiya na Afirka da Ƙungiyar AYAP ta yi bisa cancanta.
“Majalisar Matasan Afirka don Zaman Lafiya (AYAP) dai ƙungiya ce mai zaman kanta, wacce ta sadaukar da kanta don inganta zaman lafiya a fadin Afirka. Manufarmu mayar da hankali ne kan samar da yanayi na ba da dama don ƙarfafa matasa kan sana’o’i da kuma samar da zaman lafiya ta hanyar shirya laccoci da shawarwari, da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da hana sauran abubuwan da ba su dace ba da horar da matasa kan sana’o’i domin hana su zama banza Injiniya Ilyasu Usman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering Nigeria Limited, ya samu karramawa a matsayin Jakadan zaman lafiya na Afirka daga Ƙungiyar AYAP. Wannan babbar lambar yabo ta yaba da irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta zaman lafiya da ƙarfafa gwiwar matasa a Nijeriya da ma sauran ƙasashen duniya,” ta ƙarkare.
A jawabinsa Ambasada Injiniya Iliyasu Usman Salhu yayin karramawar ya nuna mutuƙar jin daɗinsa ga shugabancin ƙungiyar ta AYAP, tare da yin alƙawarin haɗa kai da su domin bunƙasa zaman lafiya da bunƙasa matasa. Ya kuma ƙarfafa gwiwar ƙungiyar da su ɓullo da tsare-tsare da za su taimaka wa matasa su tsaya wajen ƙoƙarin dogaro da kan su da kuma sanin ya kamata.
Ƙungiyar Matasan Afirka don zaman lafiya (AYAP) ta karrama Injiniya Ilyasu bisa jajircewarsa na inganta zaman lafiya da ƙarfafa matasa. Manufar AYAP ta mayar da hankali ne kan samar da yanayi masu dacewa don ci gaban matasa da samar da zaman lafiya ta hanyar ba da shawarwari, laccoci, da horar da basira.






