Daga Ibrahim Muhammad Kano
Shugaban ƙaramar hukumar Bebeji Dakta Alhassan Salisu Bebeji ya ce kasancewar mutuwa ta zama ƙaddara ga ɗan’adam, babu yadda za su yi, wannan rashi na Aminu Ɗantata sai dai su gode wa Allah, domin tasa ta yi kyau ya gama lafiya, kuma suna yi masa fatan samun rahama.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa a yayin da ya jagoranci tawaga suka kai ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata ya ce irin abin da ya yi musu ba za su iya cewa komai ba sai dai su gode wa Allah ƙaramar hukumar Bebeji tana cikin alhinini da jaje na wannan rumfa da ta faɗi tasu, domin komai da Allah ya ba su a Bebeji ya biyo ne ta ƙarƙashinsa, shi ne ya samar musu kwalta daga Gwarmai zuwa Bebeji da katafaren masallacin Idi da na Khamsul Salawati da na Sallar Juma’a da sakatariya shi ne silar samun ƙaramar hukumar.
Ya ce alfarmarsa ce tasa lokacin gwamnatin soja ta Babangida aka ba su ƙaramar hukuma bayan ma har an rufe karɓa kusan duk abin da suke a ƙaramar hukumar suna sanya sunansa ne Cibiyar koyar da sana’o’i da Asibiti da sakatariya komai nasu sunansa ne. Don haka wannan rasuwa an yi wa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoransu Kwankwaso da shi kansa shugaban ƙaramar hukumar da dukkan al’ummarsu suna alhini sosai a kai.
Dakta Alasan Salisu Bebeji ya ce idan da masu arziƙi za su yi koyi da wannan Uba nasu Alhaji Aminu Ɗantata da ƙasar nan za a sami sauƙin raɗaɗin ƙuncin rayuwa ya yi amfani da damarsa da Allah ya ba shi da dukiyarsa duk abin da Allah ya ba shi domin neman yardar Ubangiji.






