Daga Ibrahim Muhammad
Wasu daga ‘yan takarar da suka yi takarar majalisun tarayya da na jiha a ƙarƙashin jam’iyar PDP a zaɓen 2023 a jihar Kano guda 27 ƙarƙashin jagorancin Hon. AbdulRahman M. Salga sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar ADC.
Sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Kano.
AbdulRahman Salga, wanda shi ne tsohon shugaban PDP iyali ɗaya, kuma wanda ya yi takarar majalisar tarayya na PDP a ƙaramar hukumar Dala ya ce, sun yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan sun tuntuɓi magoya baya, ‘yan’uwa da abokan arziƙi.
Ya bayyana cewa daga cikin dalilansu na barin jam’iyyar PDP shi ne na yawan samun rigimar cikin gida da ta addabi jam’iyyar sakamakon akwai waɗanda suka maƙale a ciki suke kunna wutar rikicin da suke cin gajiyar hakan saboda sun ɗauki hakan sana’a.
Hon. AbdulRahman M. Salga ya ce su a tafiyarsu ta siyasa suna yi ne domin kishin nema wa al’umma mafita, musamman talakawa daga halin matsi da suke ciki. Don haka a matsayinsu na ‘yan takara suka amince su bar jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar ADC.
Mainasara ya ce komawarsu ADC zai ba su damar gudanar da siyasa ta kishi da ‘yanci ta nema wa al’ummar ƙasar nan mafita, kuma nan gaba kaɗan akwai gagarumin gangamin jam’iyyar ADC da za su gudanar a jihar Kano.






