Ginin Kasuwar Waya ta Jawwala da Gwamnatin Kano Ke Yi Zai Kara Samar Da Aikin Yi Ga Matasa -Sakataren Kasuwar

Daga Ibrahim Muhammad.

‘Yan kasuwar Jawwala sun bayyana jin daɗinsu kan gina musu sabuwar kasuwar da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf take da cewa hakan zai ƙara taimakawa wajen samawa dimbin matasa aikin yi da bunƙasa harkokin kasuwanci.

Sakataren kasuwar waya ta Jawwala da ke Kano, Musa Balarabe Bello ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida game da aikin ginin da ake na sabunta kasuwar, ya yi nuni da cewa ita dama tun asali kasuwar an gina ta ne a lokacin gwamnatin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso a wajen da take domin hana kawar da ɓata-gari da suke taruwa a wajen aka raya wajen.

Ya ce a wancan lokacin irin kyawawan manufar Kwankwaso ta gina matasa a kan sana’a ta sa aka sami matashi Kamalu Mai Jawwala, wanda shi ne shugaban kasuwar ya jajirce, ya yi ƙoƙari aka tabbatar da gina kasuwar tun farko, haka ma a wannan lokaci ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir ya jajirce domin sake gina kasuwar, ƙawata ta da gini na zamani, ta yadda ɗimbin matasa za su amfana.

Ya ƙara da cewa yanzu haka ana gina ɓangaren farko ne na rukunin kasuwar, domin kasuwar a yadda take a baya ta cika dama makil da jama’a da aƙalla mutum 1,500 ke harkokin sana’ar saye da sayar da waya da kayyaykinta da ma masu gyara, yanzu kuwa suna sa rai idan aka kammala ginin za ta ɗauki mutum 10,000.

A baya shagunansu na gini a kasuwar guda 25 ne, yanzu kuwa kusan guda 305 zai zama, wannan babban cigaba ne ga kasuwar.

Sakataren kasuwar waya na Jawwala ya ce kodayaushe abin da tsarin jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yake ƙarfafa shugaban Kasuwar Alhaji Kamalu Mai Jawwala a kai shi ne na nema wa al’ummarsa cigaba.

Don haka ya jajirce don tabbatar da aikin gina kasuwar da ake yi yana tafiya cikin nasara, in ji shi.

Ya ce nasarar aikin na tattare ne da gudunmuwar mutum uku, jagora Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma shugaban kasuwar, Alhaji Kamalu mai Jawwala sakamakon irin jajircewar sa ta taimaka ta haifar da wannan alheri.

Ya yi nuni da cewa duk abin da ya taso ba yadda za a yi a ce kowa ya fahimci amfanin abin, amma idan na alkhari ne sannu a hankali kowa zai fahimta, kuma yanzu ‘yan kasuwar Jawwala kaso 70 cikin 100 sun fahimci gina kasuwar cigaba ne a gare su. Kuma ginin da ake babu wani gini da a dukkan gine-gine da ke kewayen wajen da ya kai na kasuwar Jawwala da ake tsari mai kyau da nagarta da inganci.

Musa Balarabe Bello sakataren kasuwar wayar na Jawwala ya yi kira ga ‘yan kasuwar su cigaba da kwantar da hankalinsu da bai wa shugaban kasuwar Kamalu mai Jawwala haɗin kai da goyon baya a ƙoƙarinsa na ganin cigabansu, suna kuma sa ran nan da ɗan lokaci kaɗan za a kammala gina rukunin kasuwar kashi na farko da ake yi.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength