Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnatin jihar Kano ta yaba da taron makon dokoki da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo ta jihar Kano, ta shirya mai taken DOKA DA ODA A DEMOKWARAƊIYYA da cewa taro ne mai muhimmanci na ƙarfafa gwiwa da ya zo daidai a kan gaba na matsayar shari’a da demokwaradiyya.
Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Faruƙ Ibrahim ne ya bayyana hakan a taron da aka gudanar na makon lauyoyi.
Ya ce ƙungiyar lauyoyi sun kyauta ƙwarai da zaƙar taken taron na dokoki na demokwaraɗiyya da kuma gudanar da shi a Kano, wacce jiha ce Cibiya ta Shari’a da Demokwaraɗiyya.
Ya ƙara gode wa ƙungiyar lauyoyin reshen Ungogo da suka yi wannan tunani mai zurfi, domin ana buƙatar abubuwa da aka tattaunawa a taron su zama matashiya ne ga lauyoyi da Alƙalai da ‘yan siyasa domin su kyautata ayyukansu yadda za a sami cigaba a Kano da ƙasa baki ɗaya.
Sakataren Gwamnatin na jihar Kano ya ce Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf tana ƙoƙari matuƙa a fannin Shari’a, domin ba ya jin an taɓa samun wata gwamnati a Kano da ta yi irin hoɓɓasa, da yunƙuri mai ƙarfi wajen inganta harkokin Shari’a kamar ta.
Ya ce daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin jihar Kano na kyautata harkar Shari’a ba da jimawa ba aka ɗauki sabbin lauyoyi matasa da suka gama ma’aikata guda 70 aka sa su a Ma’aikatar Shari’a bisa la’akari da cewa nauyi ya yi wa wanda suke ciki yawa ga shekaru wasu na yin ritaya don haka aka ga dacewar ɗaukar matasa maza da mata domin su sami horo na ƙwarewa kamar yadda magabata suke da ƙwarewa domin maye gurbinsu in sun bar aiki.
Alhaji Umar Faruƙ Ibrahim ya ƙara da cewa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na kokari wajen yaƙi da cin hanci da rashawa kwanan nan aka naɗa sabon shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa don maye gurbin wanda ya kammala wa’adinsa.
Ya ce akwai matakai da dama da Gwamnatin jihar Kano ke ɗauka wajen kyautata harkokin Shari’a. Don haka ya yi kira ga mahalarta taron makon dokoki da ƙungiyar lauyoyi reshen Ungogo suka gudanar su yi amfani da irin jawabai da aka gudanar domin kyautata aikinsu yadda zai amfani jihar Kano da sauran al’ummar ƙasar nan.
A nasa jawabin Antoni janar, Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Barista Haruna Isan Dederi, wanda ya sami wakilcin Husaini Hasam Sulaiman ya ce Gwamnati tana mutuƙar farin ciki da irin waɗannan tarurruka da ake yi don ƙarfafa tsarin dokokin Shari’a, kuma kasancewar dokokin ana so duk ɗan ƙasa kowa ya zama yana ƙarƙashin bin dokar ƙasa tun daga kan mai mulki har wanda ake mulka babu zaɓi.
Ya ce ba da jimawa ba ma Gwamnatin jihar Kano ta kafa hukumar “social protection agency” Da naɗa shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci na Kano duk wannan ƙoƙarin Gwamnati ne na tabbatar da dokoki ga kuma ‘yancin kai da ake bai wa Shari’a da duk abin da ya dace.
Hussaini Hassan Sulaiman ya ce ana ƙoƙarin wajen nema wa mutane da ake tsarewa ba da haƙƙinsu ba ‘yanci ana kuma girmama dokokin kotu da kuma ƙoƙarin ganin ana gudanar da Shari’a a kan lokaci da sauran matakai da ake ɗauka don kyautata tsare dokoki.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar lauyoyi na ƙasa reshen Ungogo Kano, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce, taron na makon dokoki ne da aka saba ana gabatar da shi duk shekara da aka yi wa na bana taken doka da oda a lokacin demikwaraɗiyya.
Ya ce abin da ake so a cimma na dalilin taron shi ne a wayar da kan jama’a gaba ɗaya da lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki a kan yaya doka take tafiya ƙarƙashin ɗemokwaraɗiyya me kuma ɓangarorin Gwamnati ke aiwatarwa a tsarin demokwaraɗiyya shi ya sa ma suka gayyaci wasu daga jami’an Gwamnatin jihar Kano taron domin yin ƙarin haske kan abin da Gwamnati take kan kiyaye dokoki.
Shugaban ƙungiyar lauyoyi na ƙasa reshen Ungogo ya yi nuni da cewa daga irin matsaloli da lauyoyi ke fuskanta ba ya wuce na yanayin aiki da abokan aiki shi ya sa suka gayyaci ɓangarori daban-daban da suka haɗa da jami’an tsaro don fahimtar juna a kan harkar tsaro da na haƙƙoƙin ɗan’adam ƙarƙashin tsarin demokwaraɗiyya.
Ya yaba da irin ƙoƙarin da Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ke yi wajen harkar inganta Shari’a sai dai suna ƙara kira a kan Gwamnatin ta cigaba da bai wa harkar Shari’a kulawa ta musamman.
Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya bayyana mutuƙar gamsuwa da yadda lauyoyi da dama tun daga kan mambobinsu na reshen Ungogo da sauran rassan ƙungiyar na Kano da wasu da suka zo daga Bauchi, Zariya, Gombe, Kaduna, Dutse da sauran wurare da yawa sun yi farin ciki da hakan.
Ya yi fatan za su koyi darussa daga takardu da mukaloli da aka gabatar a kan harkar doka da oda ƙarƙashin demokwaraɗiyya.







