Daga Ibrahim Muhammad
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Hasssn Shehu Husaini a ƙoƙarinsa na kyautatawa magoya baya, ya gudanar rabo kashi-kashi ga ɗimbin al’umma da suka amfana a matakai daban-daban.
Daga irin rabon tallafin da ɗan majalisar ya gudanar ya haɗa da bai wa matasa ‘yan Social Media guda 150 tallafin kuɗi N40,000 kowanne ɗaya daga cikinsu.

Hon. Hassan Shehu Husain ya kuma rabawa shugannin jam’iyya na option A da B a matakin ƙaramar hukumar Nasarawa N25,000. Na matakin mazaɓu 11 kowanne N10,000.

Haka kuma ya yi rabon mashinan hawa guda 38 ga ‘yan gwagwarmaya na mazaɓu 11, tare da raba wa su ma mata ‘yan gwagwaraya daga mazaɓu 11 na ƙaramar hukumar kekunan ɗinkin guda 40.

Wakilin na ƙaramar hukumar Nasarawa a Majalisar Tarayya ya ƙara da raba wa ‘yan gwagwarmaya mashinan hawa guda 16 da na’ura mai ƙwaƙwalwa da aka fi sani da laptop guda 15.

Hon. Hassan Shehu Hussain wakilin ƙaramar hukumar Nasarawa a Majalisar Wakilai na Tarayyar ya ƙara da bai wa wasu ‘yan gwagwarmayar wayar hannu ƙirar Redmi 14c guda 50.
Shi ma shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukuma Nasarawa ya sami kyautar motar hawa ƙirar lexus 350.

Cikin ƙarin waɗanda suka amfana da tagomashin na ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa a Majalisar Tarayya Hon. Hassan Shehu Hussain sun haɗa da shugabannin COCUS da na lafiya jari da na CRC da Kano Propa da Kwankwasiyya Movement na matakin ƙaramar hukumar.

Hon. Muhammad Adamu Bomboy jigo ne a tafiyar Kwankwasiyya a mazaɓar Gama, kuma ɗaya daga jagorori na tafiyar Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Nasarawa, ya bayyana godiya ga Allah da ya ba su jajirtaccen ɗan Majalisar Tarayya, Hon. Hassan Shehu Husain bisa sahalewar jagoransu na Kwankwasiyya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, tare da gudunmawa na Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ya ƙara da cewa babu abin da za su ce da ɗan Majalisar Tarayyar na Nasarawa sai godiya, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu, domin a ƙasa da watanni 48 zuwa 50, ya gudanar da ayyuka da dama da suke taɓa zukatan al’umma.
Sannan ya zo a cikin wannan wata na Agusta ya yi abubuwa da yawa na tallafi, kama daga tallafa wa ‘yan Social Media da shugabannin jam’iyya tun daga matakin mazaɓu zuwa ƙaramar hukuma da Coucos da sauran ‘yan jam’iyya maza da mata matasa da shugaban jam’iyya.

Hon. Muhammad Adamu ya ce wannan tallafi da ɗab majalisar yake yi na ɗaiɗaikun mutane a kullum da na ƙungiyoyin al’umma, kari ne a kan irin ɗimbin ayyuka yake gudanarwa, kama da lga kai ƙudirin masu muhimmanci Majalisa da hanyoyi da yake da sauran abubuwa da dama da ake gani a ƙasa a bayyane.
Don haka, Hon. Muhammad Adamu Bomboy yi kira ga dukkan waɗanda suka ba da gudunmawa a wannan tafiya ta ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa da tsarin Kwankwasiyya da layi bai zo kansu ba, su ƙara haƙuri da cigaba da ba shi goyon baya da yardar Allah za su mori wannan tafiya da ake yi.






