Daga Ibrahim Muhammad
Kakakin Majalisar Kansiloli na ƙaramar hukumar Fagge, ya gudanar da taron buɗe rukunin ginin banɗakuna na zamani da ya gina a mazaɓarsa kusa da masallacin Marigayi Sheikh Muntari Atamma.
A yayin ƙaddamar da banɗakunan ya ce, yana godiya ga Allah da ya nuna masu soma aikin da kammala shi, zuwa ƙaddamar da shi da ya yi a ranar Juma’ar nan.
Wuri ne da ya ƙaddamar na banɗakuna guda biyar da suka ƙunshi ɗakin wanka da na bahaya da kuma sauran guda uku da aka keɓe su ga kowa da kowa da za a yi amfani da su saboda sirrantawa, domin akwai masallaci a gefe da babu wurin kama ruwa a ciki kuma hanya ce ta ‘yan kasuwa da ya kasance tun daga Plaza babu inda za a sami makewayi sai wannan da ya yi bisa sahalewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce su je a duba buƙata ta jama’a na ƙasa, abin da suke so a yi musu wannan na daga abin da jama’a ke so shi ya sa suka gina banɗakuna da kowa ke murna da su.
Hon. Sani Scorer ya ce bayan haka ya gina mita 800 na kwalbati a bayan wujen tare da rufe shi gaba ɗaya. Wannan abin jin daɗi ne gare shi da jama’ar da suke mulka kuma yana daga ayyuka da aka kammala a cikin wata takwas da zuwa su karagar mulki.

Bayan wannan akwai kwalbatoci da gadoji kusan huɗu da duka sun lalace suka sa aka fasa su suka yi musu aiki mai ƙwari da rodi mai ƙarfin 16 MM ko tirela ce da kaya ta hau ba za ta fashe ba, suna so kamar yadda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yake aiki mai inganci haka suke koyi da shi, kowa na murna da aiki, kuma aikin da suke tamkar farawa aka yi. Za a cigaba da yi a fannoni da dama.
Ya ce kamar yadda suke tare da shugabanninsu na matakin ƙaramar hukuma a siyasa, jagoransu ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar6 hukumar Fagge, Batista Muhammad Bello Shehu, wanda ba ya ƙwange a aikinsa, zuwa yake ya zaƙulo ayyuka daga Gwamnatin Tarayyar, ya kawo ƙaramar hukuma yana aiwatarwa, domin a tsarin su na Kwankwasiyya taimako ne ga al’umma kamar yadda Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ɗora su a kai, kuma haka suke tafiya a kai.
Ya ƙara da cewa wannan banɗakuna da suka yi akwai mutane ‘yan kwamitin masallacin Marigayi Sheikh Muntari Atamma da suke kula da wajen, akwai teloli a kewayen wajen an ba su makulli haka Alaramomi da sauran mutane da za su wakilci sauran mutane su ma an ba su makullan wajen, saboda kulawa da masu shiga da fita domin kiyaye tsafta kuma duk ciki akwai famfo da ruwa awa 24 a wajen bayaha da na wanka, sannan akwai mutum da za a ajiye mai kula da tsaftace banɗakunan za a riƙa ba shi alawus duk wata har tsawon lokacin wa’adinsu na mulki ya yi.
Kakakin Majalisar Kansilolin na ƙaramar hukumar Fagge ya ƙara da cewa akwai ayyuka da za su bijiro da su da dama da suka haɗa da yin kwalbatoci da gyaran makarantu da za a yi a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Masu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sahale a yi a dukkan mazaɓu ƙaramar hukumar Fagge.
Irin waɗannan ayyuka da ake yi yana yi wa jama’a daɗi suna samun natsuwa a kan zaɓen da suka yi.
Hon. Sani Muhammad Scorer, Kansila mai wakiltar mazaɓar Fagge D1 ya ce, tunda aka kafa Kano ake mulkin farar hula babu wani Gwamna a jihar Kano da ya yi tunani mai kyau na kai abubuwa lungu da saƙo irin Gwamna Abba Kabir Yusuf, saboda ya san duk zaɓe da ake a mazaɓa ake yi.
“Mazaɓa kuma ta Kansila ce, shi ya sa ya ba Kansiloli dama suke aiki, ranar da za a fito za a yi yaƙin neman zaɓe da ranar zaɓe duk wanda ya fito ya san an yi aiki, zuwa zai yi ya damgwala ƙuri’a ga Abba kuma kujerar Gwamna 2027 ɗauki -dora ce, nasara ce ga NNPP ta Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf saboda an yi aiki a ƙasa,” in ji shi.
Hajiya Rahama Kabir Fagge Babbar mai ɗaukar wa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf rahotanni na musamman a fadar gwamnatin jihar Kano ɗaya daga cikin manyan baki a yayin taron
ta ce wannan aiki tun soma shi suka zo suka gani, wuri ne da a baya don wani kewaye da bulo bai fi ɗori biyu ba, sai don kwano da aka katange, amma yanzu Kansilan Fagge D1 Kakakin Majalisar Kansilolin ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Muhammad Sani Scorer bisa sahlewar da Gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi wa kansilolin mazaɓun jihar Kano 480 na ƙananan hukumomi 44 su aiwatar da ayyukan a mazaɓu ya fitar da samfur na gina wannan katafaren banɗakuna mai kyau da tsari.
Ta yi nuni da cewa Kakakin kansilolin Fagge ya zuba banɗakuna biyar ginin zamani an kewaye rijiya da yin matakala da mutane za su taka su shiga an samar da fanfuna na ruwa a ciki da wajen banɗakunan da aka yi daga hagun masallacin Sheikh Marigayi Muntari Atamma da yake a dama da shi wanda ‘yan kasuwa da suke wucewa da alarammomi da sauran al’umma za su amfana cikin jin daɗi. Sannan ga kwata mai tsawon da aka yi aka rufe baya ga wasu ayyuka da Kansilan yake da dama na gyaran makarantu da magudanan ruwa.
Babbar mai rahoton a fadar gwamnatin Kano, Rahama Kabir Fagge ta ce, babu abin da za su ce da tafiyar Kwankwasiyya da mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf sai godiya ga Allah, domin a shekara biyu ya fitar da Kwankwasiyya kunya, duk inda aka duba za a ga dashen ta na alheri. Kuma Hon. Sani Muhammad Scorer ya ƙara musu jin daɗi da alfahari da ayyukan gwamnatin Kwankwasiyya da Abba Gida Gida da ake a Fagge da jihar Kano gaba ɗaya.
Ta yi kira ga al’umma su kula da banɗakuna da aka yi don sama musu sauƙi wajen biyan buƙatunmu na tsaftace wajen.
Shi ma a nasa jawabin, limamin masallacin Sheikh Marigayi Muntari Atamma, Malam Hashimu Abdulkarim ya gode wa Hon. Sani Scorer bisa samar da waɗannan banɗakuna da ya yi. Ya yi addu’ar Allah ya ƙara kiyaye gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Limamin Malam Hashimu Abdulkarim ya ce a baya wurin ƙuntatacce ne, yanzu an mutunta su, an kyautata musu, an yi gini na zamani, an sa fanfuna da ruwa a wadace za su yi ƙoƙari wajen ganin sun kula da shi da yardar Allah.







